Bidiyon Yaron Dake Talla Mai Sarrafa Lissafi Kamar Kwamfuyuta Ya Bada Mamaki

Bidiyon Yaron Dake Talla Mai Sarrafa Lissafi Kamar Kwamfuyuta Ya Bada Mamaki

  • Wani matashin yaro mai talla ya taba zukatan jama’a a soshiyal midiya da irin baiwar da yake da ita ta lissafi mai bayar da mamaki
  • A wani bidiyo da aka gani a Instagram, yaron yana watsatsala lissafi tare da bayar da amsa cikin dakika kadan ba tare da dadewa ba
  • Ma’abota amfani da soshiyal midiya suna tambayar dalilin da yasa yaron ke yawon talla a maimakon ya kasance a makaranta

Ma’abota amfani da instagram sun sha mamaki kan baiwar da wani matashin mai talla yake da ita a fannin lissafi.

Yaro mai talla dake lissafi
Bidiyon Yaron Dake Talla Mai Sarrafa Lissafi Kamar Kwamfuyuta Ya Bada Mamaki. Hoto daga @instablog9ja
Asali: Instagram

A wani bidiyo da ya yadu yanzu a Instagram, yaron ya tsaya kusa da wasu jama’a wadanda suka tsayar da shi a tsakar titi yayin da yake talla.

A hanzarce yake ta bada ansar tambayoyin lissafi da aka yi masa. Da yawansu sun dinga mamaki kan yadda ansa ke hanzarin fitowa daga bakin yaron.

Kara karanta wannan

Bidiyon Shigar Ango Wurin Shagalin Aurensa a Akwatin Gawa Ya Gigita Amarya

Yana amsa tambayoyin lissafi babu sassauci

Abu mafi bayar da sha’awa shi ne yadda yaron baya ko amfani da kalkuleta, lamarin da yasa jama’a suka dinga tambayar dalilin da yasa baya makaranta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Babu tabbacin cewa yaron talla yake yi dindindin ko kuma yana zuwa makaranta.

Kalla bidiyon matashin yaron:

Ma’abota amfani da Instagram sun yi martani

@familydoctor_blog yace:

“Allah me yasa yaro kamar wannan zai kasance a titi yana talla? Allah ka albarkace ni, ina son daukar nauyin karatunsa har digirin digirgir. Ubangiji ka saka min albarka. In har na ga masu hazaka da basu da dama ko yara masu kokari kamar wannan dake kan titi yana talla, yana sanya min wani nauyi a zuciyata na tsawon ranar ba zan kasance daidai ba.
“Ubangiji ya turowa yaron nan mai taimako kada rayuwarsa ta daidaice. Amin.”

Kara karanta wannan

Bayan shiga daga ciki, ango ya yi wani gargadi mai zafi ga dukkan abokansa

@chinny_005 tayi tsokaci da:

“A gaskiya ‘dan baiwa ne, ina fatan bidiyon nan zai hada shi da mai taimakonsa. Yana bukatar wayewa ta ilimi.”

@vstarma yace:

“Allah ya bamu gwamnati tagari da zata taimakawa irin wadannan mutane.”

@muyiair yayi martani da:

“Wannan a takaice ‘dan baiwa ne yake bata lokaci a wani wuri. Na so a ce yana makaranta, idan baya zuwa zan so in taimake shi.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel