Tashin Hankali, Kofur Yayi Tatil da Giya, Ya Buge Babban Janar Har Lahira

Tashin Hankali, Kofur Yayi Tatil da Giya, Ya Buge Babban Janar Har Lahira

  • An garkame wani kofur a barikin Soja bayan sanadiyar mutuwar wani babban janar a ranar Talata
  • Majiyoyi a gidan sun bayyana cewa Janar din ya mutu sakamakon raunukan da ya samu
  • An kaddamar da bincike bincike kai tsaye kuma hotunan motar da na Kofur din sun bayyana

Legas - Diraktan harkokin kudi na cibiyar samar da muhalli ga jami’an sojojin Najeriya watau, of the Nigerian Armed Forces Resettlement Centre (NAFRC). Birgediya Janar O.A James ya rigamu gidan gaskiya.

Babban Janar din ya mutu ne da daren Talata bayan wani karamin soja, Kofur Abayomi Ebun, wanda ake zargin yayi tatil da barasa ya bugeshi da mota, Premium Times ta ruwaito.

Rahoton ya kara da cewa lamarin ya auku ne misalin karfe 10:30 na dare yayinda Biergediya Janar James ke hanyar tafiya gidansa dake NAFRC Barracks dake Legas.

Kara karanta wannan

Yadda ‘Dan Majalisar Legas Ya Rasu Wajen Taron Kamfen Bola Tinubu a Garin Jos

Wata majiya tace:

“Janar na takawa zuwa gidansa dake cikin Bariki lokacin da wani Soja da ya bugu da giya ya hankadeshi.”
“Sojan na tukin banza cikin barikin kafin ya buge janar din.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sojaa
Tashin Hankali, Kofur Yayi Tatil da Giya, Ya Buge Babban Janar Har Lahira Hoto: Premium Times
Asali: UGC

An samu labarin cewa da wuri aka garzaya da shi asibitin NAFRC inda Likitoci suka tabbatar da mutuwarsa.

Tuni an damke Kofur din kuma an kaddamar da bincike kan lamarin.

Har yanzu hukumar Soji batayi tsokaci kai ba duk da yunkurin jin ta bakin Kakakinta, Birgediya Janar Onyeama Nwachukwu.

Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Matar Kwamandan NSCDC A Nasarawa

A wani labarin kuwa,Yan bindiga sun sace matar Kwamandan sashen leken asiri na shugaban hukumar Sibil Defens, DC Apollos Dandaura, a garin Lafiya, birnin jihar Nasarawa.

An tattaro cewa yan bindigan dauke da bindigogin AK-47 sun dira gidan matar ne suka fara harbin kan mai uwa da wabi kafin sukayi awon gaba da ita.

Kara karanta wannan

An gamu: Tinubu ya gana da CAN kan muradai da buktun Kiristocin Najeriya

Vanguard ta ruwaito cewa an yi garkuwa da ita ne a unguwar Shenge dake garin Lafian Bare-bari.

Rahoton Daily Trust yace kanin kwamandan wanda shima jami'an hukumar NSCDC ne ya jikkata a harin.

An garzaya da shi wani asibiti don jinya raunukan da ya samu.

Kakakin hukumar yan NSCDC na jihar, Mr Jerry Victor, wanda ya tabbatar da aukuwan lamarin yace har yanzu shiru basu san inda suka kaita ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel