Zulum ya Sake Bude Mashahuriyar Kasuwar Shanu Bayan Rufeta Sama da Shekaru 6 a Borno

Zulum ya Sake Bude Mashahuriyar Kasuwar Shanu Bayan Rufeta Sama da Shekaru 6 a Borno

  • Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno ya sake bude shahararriyar kasuwar shanu ta Gamboru dake karamar hukumar Ngala ta jihar Borno
  • A yayin sake bude kasuwar da tayi sama da shekaru shida a garkame, Zulum ya yabawa Buhari da masu ruwa da tsaki da suka kawo zaman lafiya
  • Zulum ya ja kunnen ‘yan kasuwan shanun kan zagon kasa inda yace duk wanda aka kama da hakan zai fuskanci matsanancin fushin hukuma

Borno - Babagana Zulum, Gwamnan jihar Borno ya sake bude babbar kasuwar Gamboru ta shanu a karamar hukumar Ngala ta jihar, jaridar TheCable ta rahoto.

Kasuwar Shanu
Zulum ya Sake Bude Mashahuriyar Kasuwar Shanu Bayan Rufeta Sama da Shekaru 6 a Borno. Hoto daga TheCable.ng
Asali: UGC

Gwamnatin jihar Borno a shekarar 2016 ta rufe kasuwar saboda dakile al’amuran ta’addanci wanda ‘yan ta’addan ke samun kudi ta hanyar satar shanu da siyarwa.

Jawabin Gwamna Zulum

Kara karanta wannan

Rayuka 7 Sun Salwanta a Arangamar Sojoji da ‘Yan Bindiga a Kauyen Gwamnan Anambra

Zagazola Makama sun rahoto cewa, a yayin jawabi wurin bude kasuwar a ranar Asabar, Zulum ya shawarci mazauna yankin da ‘yan kasuwa da su guji duk wasu lamurran da zasu kara hura wutar ta’addanci a yankin.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Ina son in jinjinawa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, jami’an tsaro da dukkan masu ruwa da tsaki a kan goyon bayansu da sadaukarwarsu wurin yaki da Boko Haram da sauran miyagun lamurran da suka kawo zaman lafiya da yanzu muke fuskanta a jihar da arewa maso gabas baki daya.”

- Yace.

“Ina farin cikin kaddamar da sake bude kasuwar shanu ta Gamboru Ngala wacce aka rufe sama da shekaru shida tun farkon ta’addancin Boko Haram.
“Yayin da kuka koma safarar shanu daga Ngala zuwa Maiduguri da sauran sassan kasar nan, ina son jan kunne ga ‘yan kasuwar shanun da masu ruwa da tsaki da su guji duk wasu al’amuran zagon kasa.

Kara karanta wannan

Don Ingata Ayyukansu: Gwamnan Wata Jahar Arewa Ya Sakarwa Yan Hisbah Kudi Naira Miliyan 50

“A matsayinmu na gwamnati, zamu goyi bayan kasuwancinku amma zaku hada kai da jami’an tsaro saboda duk wanda aka kama da laifi zai fuskanci fushin hukuma.”

Gwamnati ta rufe wasu kasuwanni da tituna a Borno

Tun bayan bullar ta’addancin Boko Haram a yankin arewa maso gabas, gwamnatin jihar tayi kokarin dakile hakan ta hanyar rufe wasu kasuwanni da titunan jihar.

Daga baya bayan nan da zaman lafiya ya dawo yankin ne ake cigaba da bude titunan da kasuwanni a fadin jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel