Gwamnatin Kebbi Ta Amince Da Sakarwa Hukumar Hisbah Kudi Miliyan N50

Gwamnatin Kebbi Ta Amince Da Sakarwa Hukumar Hisbah Kudi Miliyan N50

  • Gwamnatin jihar Kebbi karkashin Gwamna Atiku Bagudu ta amince da baiwa hukumar Hisbah kudi naira miliyan 50
  • Manufar sakin wannan kudi shine don inganta ayyukan hukumar Hisbah wacce ke yakar rashin da'a da gyara zamantakewar al'umma a jihar ta Kebbi
  • Gwamna Bagudu ya yaba da irin gudunmawar da jami'an shari'an ke bayarwa a fadin jihar

Kebbi - Gwamnan jihar Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu, ya amince da sakarwa hukumar Hisbah reshen jihar Kebbi zunzurutun kudi naira miliyan 50, jaridar The Sun ta rahoton.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun babban sakataren gwamnatin jihar, Babale Umar Yauri kuma aka gabatarwa manema labarai a Birnin Kebbi, babban birninin jihar.

Atiku Bagudu
Gwamnatin Kebbi Ta Amince Da Sakarwa Hukumar Hisbah Kudi Miliyan N50 Hoto: Leadership
Asali: Facebook

Manufar gwamnatin Bagudu na sakin kudin

Kamar yadda sanarwar ta bayyana, an saki kudin ne domin cika alkawarin da gwamnan ya dauka a wajen bikin cikar hukumar shekaru 20 da kudin tallafi.

Kara karanta wannan

Yadda Wata Budurwa Yar Shekara 18 Ta Kashe Jaririnta Da Wuka Bisa Shawarar Mahaifiyarta Yar Shekara 60

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sanarwar ta kuma ce gwamnan ya yi wannan karamcin ne da nufin inganta ayyukan yan Hisbah da kuma la’akari da irin gagarumin gudunmawar da hukumar ke bayarwa ta bangaren jin dadin zamantakewar jama’a da yaki da rashin da’a, rahoton jaridar Leadership.

Yan Hisba a Kano sun damke marabata, 931, ta zargi wasunsu da yin basaja da bara don leken asiri

A wani labarin kuma, mun kawo a baya cewa yan sandan Hisbah reshen Kano sun cika hannu da mabarata 931 cikin mako biyu kacal a kokarinta na raba masu bara da titunan jihar.

Kamar yadda hukumar ta Hisbah ta yi zargi, ta ce ana amfani da wasunsu a matsayin masu leken asiri wanda babban barazana ce ga zaman lafiyar jihar.

Muhammad Harun Ibn Sina, shugaban Hisbah a Kano shine ya sanar da hakan ga manema labarai a lokacin da yake koro jawabai kan ayyukan jami’ansa.

Kara karanta wannan

Rabin Albashi: Badaru Ya Bayyana Kokarin da Suke Tsakanin ASUU da FG

Ibn Sina ya ce wasu na basaja da harkar bara wajen aiwatar da miyagun ayyuka.

Hakazalika ya bayyana cewa daga cikin tanadin da aka yi. za a tura mabaratan da ba a san asalinsu ba zuwa makarantun sauya tunani da gyara hali, sannan wadanda ba a yan jihar ba za a mayar da su jihohinsu.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel