Adamawa: ‘Yan Sanda Sun Damke Wanda Ake Zargi da ATM 10

Adamawa: ‘Yan Sanda Sun Damke Wanda Ake Zargi da ATM 10

  • Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa sun yi ram da wani matashi da ake zargi da zama ‘dan damfara a kan hanyarsa ta zuwa Yola
  • An kama matashin mai suna Joseph Nwakibe da katinan ATM guda 10 na bankuna daban-daban wadanda suke damfarar mutane da su
  • An gano cewa suna hawa layi kamar kwastomin bankin yayin da suke musayar kati ga wadanda suka nemi a taimake su sannan su hada da lambar katin don damfara

Adamawa - Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta damke wani da ake zargi da zama ‘dan damfara mai suna Joseph Nwakibe wanda wani abokinsa mai suna Obinna Ajima ya gayyata a Yola domin aiwatar da lamurran ta’addanci.

Katikan ATM
Adamawa: ‘Yan Sanda Sun Damke Wanda Ake Zargi da ATM 10. Hoto daga punchng.com
Asali: UGC

Yadda aka yi ram da Nwakibe Joseph

‘Yan Sanda sun ce Nwakibe an kama shi da katinan ATM guda 10 da aka gama aiki da su wanda ake zargin ana damfara dasu, jaridar Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

Soyayya Ruwan Zuma, Yadda Wata Budurwa Ta Fada Tekun Lagas Akan Saurayi

An bayyana hakan ne a wata takarda da rundunar ‘yan sandan suka fitar a ranar Juma’a wacce kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Suleiman Yahaya, jaridar Daily Nigerian ta rahoto.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yadda matashin ke aiwatar da damfara

Wani sashi na takardar yace:

“Binciken farko ya bayyana cewa wadanda ake zargin suna yawo da katin ATM da aka gama amfani da shi na bankuna daban-daban sannan su jira wadanda zasu damfara.
“Su kan hau layi a bayan kwastomomi inda suke yi kamar zasu cire kudi sai su nemi taimakon duk wanda suka lura yana wahala wurin cire kudin.
“A yayin hakan, sai su gane lambobin katin mutum sannan su yi masa musaya da lalatacce irin na bankinsa.
“Kwamishinan ‘yan sanda CP SK Akande yayin yabawa kokarin jami’an da suka damke irin wadannan ‘yan ta’addan, ya umarci cewa a tsananta kokari wurin kama dayan wanda ake zargin.

Kara karanta wannan

Mutane Na Cigaba da Fito da Kudin da Suka Boye, An Gano N200 da Aka Buga Tun 2003

“Kwamishinan ‘yan sandan ya shawarci jama’a da su zama masu lura da kuma gujewa karbar taimako daga miyagu yayin da suke abubuwan da suka shafi bankunansu inda yace babu dalilin da zai sa a nemi taimako daga wanda ba a sani ba.
“A maimakon hakan a nemi taimakon jami’an tsaron bankin da aka je domin gujewa bata gari.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel