Jerin Sunayen Kwamishinonin ‘Yan Sanda 8 da aka Sauyawa Wurin Aiki

Jerin Sunayen Kwamishinonin ‘Yan Sanda 8 da aka Sauyawa Wurin Aiki

 • IGP Alkali Usman Baba, Sifeta janar na ‘yan sandan Najeriya ya aminta da sauyawa kwamishinonin ‘yan sandan Najeriya 8 wurin aiki
 • Kamar yadda rundunar ta bayyana, an yi hakan ne domin karfafa aikin tare da tabbatar da shugabanci nagari a cikin aikin ‘yan sandan
 • Kakakin rundunar, Muyiwa Adejobi, ya musanta labaran da ake yadawa kan cewa an canzawa kwamishinan ‘yan sandan Kano wurin aiki kan rashawa

FCT, Abuja - Sifeta janar na ‘yan sandan Najeriya, IGP Usman Alkali Baba, yayi umarnin sauyawa kwamishinonin ‘yan sanda takwas wurin aiki a jihohin kasar nan domin ingantuwar aiki da shugabanci.

Usman Alkali Baba
Jerin Sunayen Kwamishinonin ‘Yan Sanda 8 da aka Sauyawa Wurin Aiki. Hoto daga punchng.com
Asali: UGC

Baba yace hakan zai inganta ayyukan ‘yan sanda a fadin kasar nan kamar yadda jaridar Punch ta rahoto.

Manyan jami’an ‘yan sanda da aka sauyawa wurin aiki sun hada da:

Kara karanta wannan

Zaben Amurka: Cikakken Jerin 'Yan Najeriya Da Suka Ci Kujerun 'Yan Majalisu A Georgia, Pennsylvania, Minnesota

 1. Kwamishinan ‘yan sandan jihar Gombe - Etim Effiom
 2. Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano - Maman Dauda
 3. Kwamishinan ‘yan sandan Bauchi - Aminu Alhassan
 4. Kwamishinan CPTU Staff College Jos - Babatunde Ishola
 5. Kwamishinan X-SQUAD FCID Annex Legas - Mamman Sanda
 6. Kwamishinan ‘yan sandan FCID Annex Gombe - John Babangida
 7. Kwamishinan Safer Highway FHQ Abuja - Akinwale Adeniran
 8. Kwamishinan DFA FCID Annex Legas - Abubaka Lawal

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar The Nation ta rahoto cewa, wannan na kunshe ne a wata takarda da kakakin rundunar ‘yan sandan Najeriya, Muyiwa Adejobi ya fitar a ranar Alhamis.

Ba saboda rashawa aka sauyawa CP din Kano wurin aiki ba

Adejobi ya musanta ikirarin da ake yi na cewa an sauyawa kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano wurin aiki ne saboda zargin rashawa.

“Har ila yau, rundunar na son sanar da jama’a cewa da su yi watsi da labarin bogi da ake yadawa kan tsohon kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, Abubakar Lawal, kan cewa an sauya masa jiha ne saboda zargin rashawa.

Kara karanta wannan

Gudun Kada Ta Baci: An Yi Zaman Sulhu Tsakanin Atiku Da Kauran Bauchi

“Ana sake jaddada cewa sauya wurin aikin kwamishinonin rundunar abu ne da aka saba yi domin karfafa aikinsu tare da yada ilimi domin cigaban rundunar.”

- Yace.

An aike sabbin kwamishinonin ‘yan sanda jihohi 4 a kwanakin baya

A kwanakin bayan rundunar ‘yan sandan Najeriya ta aike sabbin Kwamishinonin ‘yan sanda jihohi hudu bayan na jihohin sun yi ritaya.

Daga ciki kuwa akwai jihohin Kano, Enugu da Zamfara.

A cikin wadanda wannan sauyin ya ritsa dasu a yanzu jihar Kano ce kadai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel