Gwamnatin Tarayya Ta Sanar da Cigaba da Sufurin Jirgin Kasa a Hanyar Kaduna-Abuja

Gwamnatin Tarayya Ta Sanar da Cigaba da Sufurin Jirgin Kasa a Hanyar Kaduna-Abuja

  • Gwamnatin tarayya tace shiri ya yi nisa na ganin an ci gaba harkokin sufurin ta jiragen kasa a Layin dogon Kaduna-Abuja
  • Ministan sufuri, Mu'azu Sambo, yace ma'aikatarsa ta ɗauki darasi bayan harin da aka kai, ta ɗauki tsauraran matakai
  • A ranar 28 ga watan Maris, wasu yan ta'adda suka kaiwa jirgin kasan farmaki, suka sace Fasinjoji bayan kashe wasu

Abuja - Ministan sufuri, Mu'azu Sambo, ga bayyana cewa a wannan watan na Nuwamba da mukee ciki ake shirin ci gaba da harkokin zirga-zirgan Jirgin ƙasa a layin dogon Kaduna zuwa Abuja.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa ba ya ga haka, gwamnati ta shirya sintirin tsaro a layin dogon na tsawon awanni 24 kowace rana da nufin kare sake kai hari.

Jirgin ƙasa.
Gwamnatin Tarayya Ta Sanar da Cigaba da Sufurin Jirgin Kasa a Hanyar Kaduna-Abuja Hoto: @channelstv
Asali: Twitter

Ministan ya sanar da haka ne a babban birnin tarayya Abuja yayin da yake zayyana ayyukan ma'aikatar sufuri tun daga shekarar 2015 zuwa yau.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Bude Wa Mutane Wuta a Titin Kaduna-Abuja, Sun Sace Mai Ciki Da Ɗiyarta

Yace sun shirya ingantaccen kuma isasshen tsaro domin tabbatar da tsare rayukan fasinjoji amma bai faɗi ainihin ranar da zirga-zirgan jirgin ƙasan zata ci gaba ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sambo ya ƙara da cewa ma'aikatar Sufuri ta ɗauki darasi a harin da 'yan ta'adda suka kai a watan Maris, wanda ya haddasa dakatar da Sufurin jirgin ƙasa a Titin Kaduna-Abuja.

Ministan ya sanar da cewa a yanzun an sanya wasu na'urori a Layin dogon domin sa ido kan duk wata halitta da zata gitta a kan titin, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

A cewarsa, na'urar zata bai wa shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ma'aikatu da sauran ɓangarorin da lamarin da shafa da ma hukumomin tsaro damar ganin abinda ke wakana a kan titin ba tare da jinkiri ba.

Meyasa ka dakatar da zirga-zirgan Jirgin ƙasa a hanyar?

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: Wani Jirgin Sama Ɗauke da Mutane Ya Yi Hatsari, Ya Zarce Cikin Kogi

Idan baku manta ba hukumar sufurin jiragen ƙasa (NRC) ta dakatar da harkokin sufuri a hanyar ne bayan mayaƙan Boko Haram sun farmaki Jirgi ɗauke da Fasinjoji ranar 28 ga watan Maris a Kaduna.

Yan ta'addan sun ɗana tare da tashim Bam yayin harin wanda ya yi sanadin rasa rayuka kana maharan suka yi garkuwa da Fasinjoji sama da 60. Lamarin ya ja hankalin duniya.

Sai dai maharan sun saki Fasinjojin da suka sace rukuni-rukuni, na ƙarshen sun kubuta ne ranar 5 ga watan Oktoba, 2022.

Tun kafin haka Ministan yace ba za'a cigaba da zirga-zirgan jirgin ƙasa a kan titin ba har sai baki ɗaya mutanen dake hannun 'yan ta'adda sun kuɓuta kuma an haɗa su da iyalansu.

A wani labarin kuma Bidiyon Yadda Peter Obi Ya Fusata, Ya Takali Kakakin Atiku a Wurin Mahawarar Yan Takara

Wani abu tamkar wasan kwaikwayo ya faru a wurin taron da aka shiryawa yan takarar shugaban kasa tsakanin Obi da Melaye.

Kara karanta wannan

Karshen Zamani: Yadda Wasu Matasa Suka Je Har Gida Suka Tube Wata Mata Tsirara

Lamarin dai wanda ya fara daga surutun da aka jiyo wani na yi, Peter Obi, ya nuna fushinsa kan dora laifin kan mutanensa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel