'Yan Bindiga Sun Bude Wa Motoci Wuta a Titin Abuja-Kaduna, Sun Sace Mai Ciki

'Yan Bindiga Sun Bude Wa Motoci Wuta a Titin Abuja-Kaduna, Sun Sace Mai Ciki

  • Wasu miyagun yan bindiga sun sace matar aure mai juna biyu da ɗiyarta yar budurwa a ƙauyen Akilibu dake Titin Abuja-Kaduna
  • Mazauna ƙauyen sun bayyana cewa maharan sun buɗe wa matafiya wuta kafin su ratsa ta Titin zuwa cikin jeji
  • Rahoto ya nuna cewa 'yan bindiga sun je da nufin sace mijin matar amma sai suka taras baya gida a lokacin

Kaduna - Yan bindigan daji sun yi garkuwa da wata mata mai juna biyu tare da ɗiyarta matashiya a ƙauyen Akilibu da ke kan babban Titin Kaduna zuwa Abuja.

An ce lamarin ya auku ne da misalin ƙarfe 8:30 na daren ranar Asabar da ta gabata. Maharan sun nufi gidan mutanen kai tsaye domin sace su.

Yan bindiga.
'Yan Bindiga Sun Bude Wa Motoci Wuta a Titin Abuja-Kaduna, Sun Sace Mai Ciki Hoto: dailytrust.com
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa 'yan ta'addan sun kutsa cikin gidan ne da nufin sace Mijin matar amma sai suka taras baya gidan a lokacin.

Kara karanta wannan

Karshen Zamani: Yadda Wasu Matasa Suka Je Har Gida Suka Tube Wata Mata Tsirara

Mazauna ƙauyen sun shaida wa jaridar cewa yan bindigan sun buɗe wuta da zuwansu domin tsorata mutane.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Maƙocin gidan da lamarin ya auku wanda ya nemi a ɓoye sunansa, yace maharan sun yi awon gaba da matar gidan, Adama, tare da 'yayanta huɗu amma daga baya suka sako uku.

Ya ce:

"Bamu iya bacci ba saboda harbin bindiga, sun shigo kauyen da ƙarfe 8:30 na dare lokacin mutane basu kwanta ba, kai tsaye suka tafi gidan mutumin, babban manomi amma bisa rashin sa'a ba ya gida."

Wani mazaunin ƙauyen na daban, Ashir Akilibu, yace yan fashin dajinn sun ɗauki mutanen da mamaki saboda sun zo ne tamkar jami'an tsaro.

Yan bindigan sun buɗe wa matafiya wuta

An tattaro cewa bayan sace matar da ɗiyarta, 'yan bindigan sun buɗe wa wata motar matafiya wuta lokacin da zasu keta ta kan babban Titin Kaduna-Abuja.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Bude Wa Mutane Wuta Ana Tsaka da Cin Kasuwa, Sun Tafka Barna a Jihar Arewa

Sai dai babu tabbacin ko sun haɗa da wasu matafiya a kan Titin kafin daga bisani su nausa cikin jeji.

Da aka tuntuɓi mai magana da yawun yan sandan Kaduna, DSP Mohammed Jalige, ya yi alƙawarin gudanar da bincike sannan ya sanar amma har yanzun da muke haɗa rahoton bai ce komai ba.

A wani labarin kuma Yan Bindiga Sun Bude Wa Mutane Wuta Ana Tsaka da Cin Kasuwa, Sun Tafka Barna a Jihar Zamfara

Wasu miyagun yan bindiga sun sake kai harin ta'addanci kan mutane ana tsaka da cin kasuwa a jihar Zamfara.

Wani mazaunin ƙauyen Gidan Goga da lamarin ya auku, yace mutum 2 sun mutu, maharan sun sace wasu kuma sun kona kasuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel