Wani Jirgin Sama Ɗauke Da Mutane Ya Yi Hatsari, Ya Afka Cikin Tafkin Victoria

Wani Jirgin Sama Ɗauke Da Mutane Ya Yi Hatsari, Ya Afka Cikin Tafkin Victoria

  • Wani jirgin sama ya yi Hatsari yayin sauka a ƙasar Tanzaniya, ya zarce cikin tafkin ruwan Victoria
  • Rahotanni sun bayyana cewa Jirgin ya samu tangarɗa ne sakamakon hasowar hadari da fara ruwa lokacin da zai sauka a Filin jirgin Bukoba
  • Shugabar Tanzaniya, Samia Suluhu Hassan, ta jajanta faruwar lamarin kana ta roki kowa ya kwantar da hankalinsa

Wani Jirgin sama ya yi hatsari inda ya afka cikin Tafkin Victoria dake ƙasar Tanzaniya a yayin da yake kokarin sauka a Filin sauka da tashin jirgen sama na Bukoba Airport kusa da tafkin.

Hukumar watsa labarai ta ƙasar Tanzaniya (TBC) tace zuwa yanzun an samu nasarar ceto Fasinjoji 15 da haɗarin ya rutsa da su, kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.

Jirgin da ya yi haɗari a ruwa a Tanzania.
Wani Jirgin Sama Ɗauke Da Mutane Ya Yi Hatsari, Ya Afka Cikin Tafkin Victoria Hoto: thenation
Asali: Twitter

Babu cikakken bayani kan musabbabin abinda ya haddasa hatsarin amma ma'aikatan agaji da kuma jami'an kwana-kwana sun mamaye wurim da nufin ceto mutanen dake ciki.

Kara karanta wannan

Karshen Zamani: Yadda Wasu Matasa Suka Je Har Gida Suka Tube Wata Mata Tsirara

Jaridar The Nation ta rahoto cewa Jirgin, Precision Air, ya taso ne daga Darus Salam a kan hanyarsa ta zuwa Bukoba lokacin da hadari ya haɗu ruwa ya tsuge, sakamakon haka ya faɗa cikin tafkin wanda ke kusa da Filin sauka.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar wani rahoto, wasu Hotuna dake yawo sun nuna cewa kusan baki ɗaya jirgin ya nutse kaɗan daga Fikafukin wustiyarsa ce kaɗai ta yi saura a saman ruwa.

Shugabar Tanzaniya ta yi magan kan batun

Shugabar ƙasar Tanzaniya, Samia Suluhu Hassan, ta yi kira ga masu aikin ceto da su kwantar da hankulansu kana su yi aiki a natse.

Ta ce:

"Na samu labarin hatsarin jirgin Precision Air, a tafkin Victoria da ke yankin Kagera, abun takaici ne. Ina miƙa jaje ga waɗanda wannan hatsarin ya shafa.
"Mu ci gaba da hakuri da kwantar da hankalanmu yayin da jami'ai ke koƙarin ceto Fasinjojin da abun ya rutsa da su, mu roki Allah ya taimakemu."

Kara karanta wannan

Yan Ta’adda Sun Dasa Bam Ta Karkashin Kasa a Kaduna, Mutum 2 Sun Halaka

A wani labarin kuma kun ji cewa wani Jirgin sama makare da mutane ya yi haɗari a Kasar Kamaru

Wani ƙaramin jirgin saman fasinja ya yi hatsari a wani daji da ke kudancin babbar birnin ƙasar Kamaru, Yaounde.

Ma'aikatar kula da sufuri ta ƙasar ta sanar da cewa jirgin mai ɗauke da Fasinja 11 ya yi haɗarin ne ranar Laraba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel