Ifeanyi: Yan Sanda Sun Kama Ma’aikatan Mawaki Davido Gaba Daya Kan Mutuwar Dansa

Ifeanyi: Yan Sanda Sun Kama Ma’aikatan Mawaki Davido Gaba Daya Kan Mutuwar Dansa

  • An tattaro cewa kama dukkanin ma’aikatan gidan Davido kan mutuwar dansa, Ifeanyi
  • Kakakin rundunar yan sandan jihar Lagas, Ben Hundeyin, ya tabbatar da labarin a ranar Talata, 1 ga watan Nuwamba
  • A cewar Hundeyin, ana gudanar da bincike yayin da aka tisa keyar dukkanin ma’aikatan gidan don amsa tambayoyi

Lagos - Rahotanni sun kawo cewa yan sanda sun kama dukkanin ma’aikatan gidan shahararren mawakin Najeriya, Davido kan mutuwar dansa, Ifeanyi.

Rundunar yan sandan jihar Lagas ta tabbatar da cewar dukkanin ma’aikatan na tsare a hannunsu don amsa tambayoyi, Sahara Reporters ta rahoto.

Davido da Ifeanyi
Ifeanyi: Yan Sanda Sun Kama Ma’aikatan Mawaki Davido Gaba Daya Kan Mutuwar Dansa Hoto: @davido, @yas_ln
Asali: Instagram

Kakakin rundunar yan sandan jihar Lagas, Ben Hundeyin, ya fadama manema labarai a ranar Talata, 1 ga watan Nuwamba cewa ana nan ana gudanar da bincike don gano wadanda ke da hannu a mutuwar yaron.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da aka kama mata da miji dake safarar mutane a wata jiha

Daily Post ta rahoto kakakin yan sandan yana cewa

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“An dauki ma’aikatan gidan Davido zuwa ofishin yan sanda don jin nasu bayanin kana bun da ya faru. Ba zan kira hakan kamu ba tukuna.
“Idan bayan sun bayar da nasu jawaban na abun da ya faru da kuma bayan bincike, idan aka samu wani da hannu, sai a sanya mai shi a matsayin wanda aka kama.”

Jama’a sun yi martani kan kamun ma’aikatan

ecclesiafoods:

“Ace ma’aikata 9 kuma hakan ta faru Ah!!!Ya Ubangiji, wannan abu akwai ciwo sosai…ma’aikata tara??? Wani irin sakaci ne wannan?”

seyiealabi:

“Ku kula da yaron da aka biyaka kudi a kansa sannan baku lura cewa yayi nisan kiwo ba.”

ramzychick:

“Ban taba jin irin haka ba a rayuwata gaba daya…na rasa abun yi…nima uwa ce ina tunanin yadda Chioma da davido za su dunga ji a yanzu.”

Kara karanta wannan

Matashi Dan Najeriya Ya Nunawa Duniya Kyakkyawar Budurwarsa Farar Fata Tana Rangada Masa Girki a Bidiyo

Ifeanyi Adeleke, Yaron Shahrarren Mawaki, Davido, Ya Mutu Cikin Swimming

Mun dai kawo cewa hankulan masoya mawakin Najeriya, David Adeleke wanda aka fi sani da 'Davido' sun tashi yayinda jita-jitan mutuwar dan masoyiyarsa, Chioma Rowland, ya bazu.

Rahotanni sun bayyana cewa yaron ya mutu ne cikin rafin wanka na shakatawa dake cikin gidansa dake unguwar Banana Island dake jihar Legas.

An fito da yaron dan shekara 3 daga cikin ruwan kuma aka garzaya da shi asibiti inda Likita ya tabbatar da mutuwarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng