Jami’an Hukumar Kula da Shige da Fice Sun Kama ‘Yan Kasar Waje da Katin Zabe

Jami’an Hukumar Kula da Shige da Fice Sun Kama ‘Yan Kasar Waje da Katin Zabe

  • Jami’an hukumar kula da shige da fice na Najeriya sun kama wasu ‘yan kasashen waje dauke da katikan zaben Najeriya yayin da 2023 ke gabatowa
  • Shugaban NIS reshen jihar Oyo, Isha Dansuleiman, ya sanar da cewa tuni hukumarsu ta tarkata bakin hauren ta mayar da su kasashensu
  • Ya ja kunnen wadanda ba ‘yan Kasa ba da su guji mallakar takardun da basu dace ba, zamansu a Najeriya ba yana nufin zasu iya zabe ba

Oyo - Jami’an hukumar shige da fice ta Najeriya sun kama wasu ‘yan kasar waje dauke da katikan zabe kafin zuwa gagarumin zaben 2023 a Najeriya, jaridar Punch ta rahoto.

Hukumar shige da fice
Jami’an Hukumar Kula da Shige da Fice Sun Kama ‘Yan Kasar Waje da Katin Zabe. Hoto daga punchng.com
Asali: UGC

Shugaban hukumar kwastam na jihar Oyo, Isha Dansuleiman, wanda ya sanar da hakan a Ibadan ranar Laraba a yayin taron wayar da kai da aka yi a jihar, yace kada wadanda ba ‘yan Najeriya ba su kuskure a gansu da katikan zabe.

Kara karanta wannan

Bayan Abuja, Jami'an EFCC Sun Kai Simame Shagunan Yan Canji a Jihar Kano

Yace wadanda aka kama an mayar dasu kasarsu yayin da yace ana cigaba da kama duk ‘dan kasar waje dake da takardun da bai dace ya samu ba.

Yace:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“An kama ‘yan kasar waje 18 da katikan zabe kuma a take aka mayar dasu kasashensu.
“Kada bakin haure su yi kurkuren yin zaben 2023 a kasar nan. An bar ku ku zauna a Najeriya matukar kuna da takardun da suka dace, amma hakan bai da kun zama ‘yan Najeriya ba.
“Bakin haure ba zasu iya zabe ba ko kuma a zabe su. Kada ku sake ku yi katin zabe ko karbar katin zabe kuma kada ku bari a yi amfani da ku wurin tayar da tarzoma.
“‘Yan siyasa suna da dukiya sosai da zasu yi amfani da ita, amma kada ku bari a yi amfani da ku. CGI tayi umarnin mu mayar dasu kasar su a duk lokacin da aka kama su da takardun da dokar kasa bata amince su mallake ba. Zamu mika ku ga jami’an tsaro.”

Kara karanta wannan

Sifeta Janar Ya Bayyana Dalilin Da Ya Hana Su Kamawa da Gurfanar da Tinubu

Yayi kira ga bakin haure a kasar nan da su zo su yi rijista domin gujewa tozarci.

“Ana cigaba da rijistar wadanda ba ‘yan kasa ba ta yanar gizo, ku zo ku yi rijista. Muna da injina da zasu dauka zanen hannayenku, amfanin ku ne.
“Nan babu dadewa zamu taso da karfinmu. Idan kuna tunanin kuna boyewa ne a ko ina, zamu iya zakulo ku daga ko ina.”

- Ya kara da cewa.

NIS ta kama ma’aikata ‘yan China sama da 200 a Neja ba su da biza, wasu sun tsere

A wani labari na daban, sama da ma’aikata 200 ‘yan kasar China ne da safiyar Alhamis din nan jami’an hukumar kula da shige da fice ta Najeriya suka kama a wani wurin aikin gini a jihar Neja.

‘Yan kasar Chinan da aka kama ma’aikatan kamfanin Sinohydro ne; wani kamfanin samar da wutar lantarkin kasar Sin da ke kula da aikin samar da wutar lantarki na Zungeru na $1.3bn da gwamnatin Najeriya ke aiwatarwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel