NIS ta kama ma’aikata ‘yan China sama da 200 a Neja ba su da biza, wasu sun tsere

NIS ta kama ma’aikata ‘yan China sama da 200 a Neja ba su da biza, wasu sun tsere

  • Jami'an tsaron Najeriya sun kama wasu 'yan China da suka shigo Najeriya suka yi zamansu ba tare da bizan zama ba
  • An kama su ne a wurin aikin samar da wutar lantarki da ke gudana a wani yankin jihar Neja a Arewacin Najeriya
  • Rahotannin da muka samu sun bayyana yadda aka kama su, sannan da yadda suka yi zamansu ba tare da tsangwama ba

Jihar Neja - Sama da ma’aikata 200 ‘yan kasar China ne da safiyar Alhamis din nan jami’an hukumar kula da shige da fice ta Najeriya suka kama a wani wurin aikin gini a jihar Neja.

‘Yan kasar Chinan da aka kama ma’aikatan kamfanin Sinohydro ne; wani kamfanin samar da wutar lantarkin kasar Sin da ke kula da aikin samar da wutar lantarki na Zungeru na $1.3bn da gwamnatin Najeriya ke aiwatarwa.

Yadda aka kama 'yan China ajihar Neja
Da dumi-dumi: Jami'an tsaro ma’aikata ‘yan kasar China sama da 200 a Neja bisa wasu takardu | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

An tattaro cewa ma’aikatan na kasar China da ke wurin, sun shigo Najeriya da bizar yawon bude ido na watanni shida ne.

SaharaReporters ta ruwaito cewa, ma'aikatan sun ci gaba da zama a Najeriya sama da shekaru biyu, suna aiki kuma suna samun makudan kudaden albashi ba tare da tsangwama ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yawancinsu an ce sun shigo Najeriya ne kafin barkewar cutar Korona a watan Fabrairun 2020 kuma sun ci gaba da zama duk da karewar bizarsu.

An kuma tattaro cewa yayin da jami’an shige-da-fice suka kama sama da 200 ‘yan kasar China a samamen da aka kai ranar Alhamis a wurin ginin, wasu daruruwan kuma sun tsere cikin daji don gudun kada a kama su.

Lamarin ya haifar da hargitsi a kewayen al'ummar yankin inda mazauna suka yi ta gudu don gudun kada a kama su.

Hukumar NIS ta ce:

“Yawancinsu sun shigo Najeriya ne da bizar yawon bude ido da suka kare sama da shekaru biyu da suka gabata amma sun ci gaba da aiki ba tare da wata atsangwama ba.
“Yayin da wadanda ke Najeriya a yanzu takardar bizarsu ta kare, kamfanin na ci gaba da kawo karin ma’aikata daga China wadanda su ma za su ci gaba da zama da aiki a nan da zarar takardunsu ya kare.
“Wasu daga cikin ma’aikatan da aka kama hukumar shige da fice ta tafi da su yayin da wasu kuma aka sake su amma an gargade su da su sabunta takardunsu ko kuma su bar Najeriya."

Najeriya dai na iya ba wasu 'yan kasashe takardun zama na dindindin. A kwanakin nan ma gwamnati ta ba wasu 'yan kasashe takardun zama, kamar yadda Channels Tv ta ruwaito.

Rikici ya barke tsakanin Hausawa da Yarbawa 'yan kasuwa, an kona shaguna, da dama sun jikkata

A wani labarin, mutane da dama sun raunana a ranar Litinin da yamma bayan fada ya barke tsakanin ‘yan kasuwa Yarabawa da Hausawa a fitacciyar kasuwar Lafenwa da ke cikin Abeokuta, babban birnin Jihar Ogun.

Majiyar The Punch ta tattaro bayanai akan yadda rikicin ya fara ruruwa tun yammacin Litinin har safiyar Talata wanda ya yi sanadiyyar babbaka shaguna da dama da kuma ji wa mutane da dama raunuka.

Wata majiya ta shaida yadda asalin fadan ya fara daga wani Bayerabe da Bahaushe, kafin ya zama gagarumin rikici.

Asali: Legit.ng

Online view pixel