Ana Tsaka da Tsoron Hari, Buhari Zai Yi Ganawar Gaggawa da Shugabannin Tsaro

Ana Tsaka da Tsoron Hari, Buhari Zai Yi Ganawar Gaggawa da Shugabannin Tsaro

  • Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yayi kiran taron gaggawa da dukkan shugabannin tsaron kasar nan a Abuja ranar Litinin
  • Hakan na zuwa ne yayin da ake tsaka da tsoron hare-haren ‘yan ta’adda a sassan babban birnin tarayyan da kewaye
  • Hadimin Buhari ya bayyana cewa shugaban kasan zai gana da su ne domin tsari da karfafa salon tsaron kasar nan a ranar Litinin

FCT, Abuja - A ranar Litinin shugaban kasa Muhammadu Buhari zai yi taron gaggawa da shugabannin tsaro na kasar nan.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari
Ana Tsaka da Tsoron Hari, Buhari Zai Yi Ganawar Gaggawa da Shugabannin Tsaro. Hoto daga TheCable.ng
Asali: UGC

Kamar yadda wallafar hadiminsa na musamman kan harkokin sadarwa masu dogaro da fasahar zamani, Bashir Ahmad, ta bayyana, za a yi taron a Abuja kuma yana daga cikin kokarin inganta tsaro.

“Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kira taron gaggawa kan tsaro gobe a babban birnin tarayya na Abuja domin sake dubawa da karfafa tsaro a kasar nan.

Kara karanta wannan

ACF Tayi Alkawarin Daukar Nauyin Karatun Daliban Jihar Kano

“Taron zai samu halartar ministan tsaro, shugabannin tsaro da sauran shugabanin cibiyoyin tsaro.”

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

- Wallafar tace.

Wannan kiran taron gaggawan na zuwa ne yayin da ake tsaka da tsoron hari a wasu sassan Najeriya.

Kasashe kamar su Amurka da Ingila sun baiwa ‘yan kasar su dake Najeriya shawarwarin tafiye-tafiye.

Amurka ta bukaci iyalan ma’aikatanta dake zama a Abuja da su bar birnin yayin da Ingila ta ja kunne kan tafiye-tafiye marasa tushe a babban birnin tarayyar kasar.

A yayin martani kan wannan cigaban, hukumar tsaron farin kaya, DSS tayi kira kan a kwantar da hankali yayin da shugaban kasan yace shawarin tafiya-tafiyen basu nufin hari za a kai a Abuja.

A daya bangaren, DSS ta tabbatar da samame da ta kai wani rukunin gidaje dake babban birnin tarayyan wanda a hakan ta cafke wani da ake zargi da ta’addanci.

Kara karanta wannan

Hukumar EFCC Tayi Nasarar Daure 'Yan Damfara 2, 800 a Watanni 10 a 2022

Ana Tsaka da Fargaba Kan Tsaro, Sojojin Kasa Sun Bayar da Lambobin Kiran Gaggawa

A wani labari na daban, rundunar sojin kasan Najeriya, ta bada lambobi na musamman ga ‘yan kasa domin rahoto tare da kai bayanai kan duk wata barazanar tsaro.

Rundunar sojin kasan ta Najeriya ta wallafa lambobin ne a shafinta na soshiyal midiya a ranar Juma’a.

A cikin makonni biyu da suka gabata, tsoro da damuwa sun cika zukatan jama’a bayan wasu kasashen ketare sun bada shawarwari kan barazanar kai farmakin ‘yan ta’adda a wasu sassan kasar nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel