Da Dumi-Dumi: Sojoji Sun Kama Kwamandan Yan Bindiga, Sun Kashe Mayaka 8 A Wata Jihar Arewa

Da Dumi-Dumi: Sojoji Sun Kama Kwamandan Yan Bindiga, Sun Kashe Mayaka 8 A Wata Jihar Arewa

  • Dakarun rundunar sojojin sama da na kasa sun dakile harin da wasu yan bindiga suka yi yunkurin kaiwa a yankin New Bussa da ke karamar hukumar Borgu ta jihar Neja
  • Sojojin sun halaka yan bindiga guda takwas tare da kama babban kwamandan da ya jagoranci kai harin
  • Lamarin ya afku ne a daren ranar Asabar, 29 ga watan Oktoba kamar yadda majiyoyi suka bayyana

Niger - Dakarun rundunar sojojin sama da na kasa sun kashe wasu yan bindiga guda takwas yayin da suke yunkurin kai mummunan hari kan al'umma a jihar Neja.

Jaridar Leadership ta rahoto cewa sojojin sun farmaki yan bindigar ne a lokacin da suke kokarin kaddamar da hari a New Bussa, karamar hukumar Borgu ta jihar Neja.

Kara karanta wannan

Gargadin Kai Hari: Shin Da Gaske An Dasa Bama-Bamai A Abuja? An Samu Bayanai

Sojoji
Da Dumi-Dumi: Sojoji Sun Kama Kwamandan Yan Bindiga, Sun Kashe Mayaka 8 A Wata Jihar Arewa Hoto: Daily Post
Asali: Facebook

Majiyoyi daga garin sun bayyana cewa dakarun sojin hadin gwiwar sun kuma kama kwamandan yan bindigar wanda ya jagoranci kai harin a daren ranar Asabar, 29 ga watan Oktoba.

HumAngle ta rahoto cewa sojojin sun dakile harin da maharan suka yi yunkurin kaiwa sansanin su da ke New Bussa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wata babbar majiya ta tsaro wacce ta sanar da batun harin ga HumAngle ta ce sojoji sun fafata da maharan a yayin da suke kokarin kutsa kai sansanin soji sannan suka halaka wasunsu.

Majiyar ta kuma ce sojojin sun kwato wata motar Hilux, motar Toyota Sienna da bama-bamai, bindigar harbor jirgin sama da sauransu daga hannun maharan.

Harin Babban Asibiti a Neja: 'Yan Bindiga Sun Aike Da Sakon Bukatunsu

A wani labari na daban, tsagerun ‘yan bindiga da suka sace wasu ma’aikata a babban asibitin Abdulsalami Abubakar, Gulu da ke karamar hukumar Lapai ta jihar Neja sun bukaci a biya kudin fansa domin su sako sauran mutum 9 da ke hannunsu.

Kara karanta wannan

Babu Uban Da Zai Tsigeni Daga Kujerar Shugaban PDP, Iyorcia Ayu Ya Fusata

Daily Trust ta rahoto cewa masu garkuwa da mutanen sun nemi a biya naira miliyan 10-10 kan kowani mutum daya wanda jimlar kudin zai kama naira miliyan 90.

Maharan wadanda suka yi awon gaba da mutum 15 ciki harda ma’aikatan asibitin sun sako wata mata da wasu yara saboda ba za su iya tafiya zuwa inda suke son kaiwa ba.

Wata majiya da ta magantu game da tattaunawa da ke gudana ta ce yan uwan wadanda aka sace suna fafutukar ganin sun hada kudin domin su biya tunda gwamnati ta rigada ta ce ba za ta biya kudin fansa kowa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel