Matatar Man Dangote Za Ta Fara Samar da Mai Ga Kasar Ghana da Sauran Kasashen Yammacin Afirka

Matatar Man Dangote Za Ta Fara Samar da Mai Ga Kasar Ghana da Sauran Kasashen Yammacin Afirka

  • Ghana na jiran tsammanin fara aikin matatar man Dangote da za ta ragewa kasar matsalar wahalar makamashi
  • Shugaban hukumar kula da man fetur a kasar Ghana, Mustapha Abdul-Hamid ne ya bayyana hakan a kwanan nan
  • A cewarsa, kasar Ghana za ta rage shigo da kayayyakin mai daga kasashen Turai da sauran kasashen ketare

Shigo da kayayyakin man fetur daga kasashen waje na samar da nakasu da illa ga fannin makamashi a kasar Ghana saboda yadda ake tafiyar da harkokin mai a kasar.

Kasar Ghana dai ta kasance daga jerin kasashen dake shigo da danyen man fetur tun shekarar 2010, wannan yasa take da rauni wajen tsayayyen farashin mai kasancewar shigo dashi ake daga Turai.

Business Insider ta ruwaito cewa, shugaban hukumar kula da man fetur a kasar Ghana (NPA), Mustapaha Abdul-Hamid ya ce, fara aikin matatar Dangote zai kawo sauyi sosai a fannin fetur a Ghana.

Kara karanta wannan

Malami Ya Bayyana Dalilai 4 da Yasa FG Ke Cigaba da Garkame Nnamdi Kanu

Matatar man Dangote za ta taimaki Afrika
Matatar Man Dangote Za Ta Fara Samar da Mai Ga Kasar Ghana da Sauran Kasashen Yammacin Afirka | Hoto: mediatracnet.com
Asali: UGC

A cewarsa, ta hanyar samar da ganga 650,000 na man fetur, hakan zai kawo sauyi sosai tare da rage wahalar shigo da albarkatun man fetur zuwa kasar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Da yake magana a bikin baje kolin kasuwanci karo na 16 da aka yi a Legas, Abdul-Hamid ya ce, kammala aikin matatar man Dangote zai kara adadin samar da man fetur ga kasar Ghana da ma nahiyar yammacin Afirka.

Ghana za ta gina ma'ajiyar man fetur

Hakazalika, ya yabawa gwamnatin Ghana a shirinta na kashe $60m wajen gina turken man fetur a kan fili mai girman eka 20,000 a yammacin kasar don ajiyar kayan mai, New Telegraph ta tattaro.

A cewarsa, aikin zai taimaka wajen habaka harkar mai, wanda ya hada da samar da albarkatu daban-daban na man fetur.

Amurka Ta Amince Da Ficewar 'Yan Kasarta da Ma'aikatan Ofishin Jakadancinta Daga Najeriya

Kara karanta wannan

‘Dan Chana Ya Musanta Halaka Budurwa Ummita a Gaban Kotu

A wani labarin, gwamnatin kasar Amurka ta amincewa 'yan kasar mazauna Najeriya da su fara fita daga kasar biyo bayan rahoton barazanar tsaro da hukumomin kasar suka samo, Channels Tv ta ruwaito.

A wani sakon ankararwa da kasar ta fitar a ranar Talata 25 ga watan Oktoba da yamma, ma'aikatar Amurka a Najeriya ta yi alkawarin ba da shawarwarin kariya da tsaron gaggawa ga 'yan kasar mazauna Najeriya.

Hakazalika, Amurka ta kuma shawarci 'yan kasarta dake Najeriya da su kasance masu boye kawunansu kuma su kasance a ababen zirga-zirgan kasuwanci idan suna son barin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel