Malami Ya Bayyana Dalilai 4 da Yasa FG Ke Cigaba da Garkame Nnamdi Kanu

Malami Ya Bayyana Dalilai 4 da Yasa FG Ke Cigaba da Garkame Nnamdi Kanu

  • Antoni janar na tarayya, Abubakar Malami, ya bayyana muhimman dalilai hudu da suka sa gwamnatin tarayya ba zata iya sakin Nnamdi Kanu ba duk da hukuncin kotu
  • Ministan yace za a duba tsaron kasa, diflomasiyyar kasashen ketare tare da dokokin kasar nan kafin a ce za a sake shi ya shaki iskar ‘yanci
  • Malami yace a fanni daya ne kacal ya samu nasara a shari’ar laifukan da ake zarginsa, don haka akwai sauran da dole sai an kammala sauraronsu

FCT, Abuja - Duk da hukuncin kotu da ya bukaci Najeriya ta mayar da shugaban kungiyar ‘yan awaren Biafra kasar Kenya tare da biya da diyyar N500 miliyan, gwamnatin tarayya ta ki sakinsa dogaro da wasu dalilai, Antoni Janar na tarayya kuma ministan shari’ar Najeriya, Abubakar Malami ya bayyana.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Manyan Kantunan Abuja Sun Fara Rufewa Sakamakon Labarin Cewa Za'a Kai Hari

Abubakar Malami
Malami Ya Bayyana Dalilai 4 da Yasa FG Ke Cigaba da Garkame Nnamdi Kanu. Hoto daga vanguardngr.news
Asali: UGC

Malami ya sanar da jaridar Vanguard a wata tattaunawa ta musamman a ranar Alhamis yace ba za a yi dogaro da mayar da Nnamdi Kanu ba a matsayin dalilin sakin shugaban IPOB din kan zargin laifuka da yayi wa gwamnatin tarayya.

Ministan shari’an yayi bayanin cewa gwamnati na rike da Nnamdi Kanu ne kan dalilai hudu ba wai mayar da shi kasar da aka dauko shi ba kadai.

Malami yace:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Saki ko rashin sakin Nnamdi Kanu duk aikin doka ne a wannan lamarin. A wurin yanke hukuncin a sake shi ko kada a sake shi wani abu ne na daban. A duba doka, a duba jama’a da bukatar kasa, na uku a duba tsaro sannan a duba diflomasiyyar kasashe.
“A yanzu bari in fara da batun doka. Wannan mutum ne da aka bayar da belinsa kan wasu zarginsa da ake yi. Ya tsallake belin ya tsere, wani laifin ne wannan ya sake.”

Kara karanta wannan

‘Yan Mata Sun Koka, Ana Yi Masu Aure da Tsofaffi Domin Iyayensu Su Biya Bashi

“Na biyu kan batun tsaron kasa, wannan mutum ne da ake zargi da cin amanar kasa, assasa barna, kisan kai da sauran tarzoma da suka dinga barazanar ga tsaron kasa.
“Na uku kan batun diflomasiyyar kasashen ketare, wannan mutum ne da yayi amfani da wata kasa wurin kaddamar da farmaki kan kasarsa.
“Toh wadannan dole a dube su kafin a san abin yi. Toh idan ta fannoni daban-daban aka gano abubuwan da suka hada da cin amanar kasa, kisan kai, tsallake beli da sauransu. Idan kayi nasara a kan abu daya yayin da ba a kammala sauran ba ba zai sa a sake ka ba ko a’a.”

- Ya kara da cewa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel