Bayan Mutuwar Sarkin Kazaman Duniya, an Gano Magajinsa Daga India

Bayan Mutuwar Sarkin Kazaman Duniya, an Gano Magajinsa Daga India

  • Jim kadan bayan mutuwar Amou Haji, wanda ya fi kowa kazanta a duniya aka fara tunanin wanda zai zama magajinsa
  • An tuno da wani mutumin kasar Indiya da ya shafe shekaru sama da 40 bai yi wanka ba, sai dai ya tara wuta ya yi bauta a gabanta
  • An ruwaito cewa, Amou Haji ya rasu ne bayan wanka da ya yi, saboda ya shafe shekaru bai yi wanka ba

Indiya - Bayan tabbatar da mutuwar mutumin da yafi kowa kazanta a duniya, Amou Haji, an samu wani dan kasar Indiya da ake tunanin shi ne zai zama magajinsa a wannan dabi'a ta kazanta.

Jaridar The Guardian ta ruwaito cewa, ana kyautata zaton Kailash 'Kalau' Singh ne zai maye gurbin Haji, wanda shi ma aka ce ya shafe shekaru da dama bai taba ruwa ba.

Kara karanta wannan

Mutumin da Yafi Kowa Kazanta a Duniya, Amou Hajji, Ya Rasu Yana Da Shekaru 94 a Duniya

A shekarar 2009, jaridar Hindustan Times ta ruwaito cewa, Kailash, wanda ya taso daga wani kauye dake wajen birnin Varanas, ya shafe shekaru 35 bai yi wanka ba, kusan shekaru 49 kenan zuwa yanzu.

Kailash Singh ya gaji Amou Haji, shugaban kazamai na duniya
Bayan mutuwar sarkin kazaman duniya, an gano magajinsa daga India | Hoto: imgur.com
Asali: UGC

An ruwaito cewa, wannan bawan Allah ya yanke shawarin daina wanka ne domin taimakawa wajen dakile matsalolin da kasar Indiya ke fuskanta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda kazantarsa take tafiya

Kullum yakan ki yin wanka tare da cewa, ya zabi yin 'wankan wuta'.

A cewar rahoton:

"Kullum da yamma, lokacin da 'yan kauye suka taru, Kalau... zai kunna wuta, ya sha tabar wiwi, ya tsaya da kafa daya tare da yin addu'o'insa ga ubangiji Shiva.

An kuma naqalto Kalau na cewa:

"Kamar dai amfani da ruwa ne wajen yin wanka. Wankan wuta na taimakawa wajen kashe duk wasu sinadaran cuta da jikin dan Adam."

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP: Buhari ya bani lambar yabo, da ita zan yi kamfen zaben 2023

Hakazalika, an ruwaito cewa, a baya dai Kalau ya kasance mai sana'ar siyar da kayan abinci, amma tun bayan fara kazantar tasa, mutane suka daina zuwa shagonsa.

A bangare guda, wani rahoton jaridar DailyMail ya bayyana cewa, Kalau ya kasance manomi, kafin daga bisani ya yi nisa a lamarin ibada.

Mutumin da Yafi Kowa Kazanta a Duniya, Amou Haji, Ya Rasu Yana Da Shekaru 94 a Duniya

A wani labarin, wani mutumi ‘dan asalin Kasar Iran mai Suna Amou Haji wanda aka lakabawa mutumin da yafi kowa kazanta a duniya sakamakon shekaru sama da saba’in da ya dauka baya wanka ya rasu yana da shekaru 94 a duniya a ranar Talata, Jaridar Punch ta rahoto.

Haji wanda ya kwashe shekaru babu wanka bai taba aure ba kuma ya mutu a ranar Lahadiwa kauyen Dejgah dake kudancin Fars, IRNA News suka rahoto.

Haji ya dinga gujewa yin wanka sakamakon tsoron kwanciya rashin lafiya da yake yi kamar yadda cibiyar yada labaran ta bayyana.

Kara karanta wannan

2023: Gwamnan PDP ya tona asirin APC, ya fadi mummunan abin da zai faru idan Tinubu ya ci zabe

Asali: Legit.ng

Online view pixel