Mutumin da Yafi Kowa Kazanta a Duniya, Amou Haji, Ya Rasu Yana Da Shekaru 94 a Duniya

Mutumin da Yafi Kowa Kazanta a Duniya, Amou Haji, Ya Rasu Yana Da Shekaru 94 a Duniya

  • Amou Haji, mutumin da yafi kowa kazanta a duniya ya kwanta dama yana da shekaru 94 a duniya a kasar Iran
  • Kamar yadda aka gano, Haji ya kwashe sama da shekaru 60 bai yi wanka ba saboda tsabar tsoron ruwa da yake yi da tsoron kwanciya rashin lafiya
  • Sai dai an gano cewa, a watannin da suka gabata, mazauna kauyen Dejgah dake kudancin Fars sun tirsasa Haji yin wanka

Iran - Wani mutumi ‘dan asalin Kasar Iran mai Suna Amou Haji wanda aka lakabawa mutumin da yafi kowa kazanta a duniya sakamakon shekaru sama da saba’in da ya dauka baya wanka ya rasu yana da shekaru 94 a duniya a ranar Talata, Jaridar Punch ta rahoto.

Amou Haji
Mutumin da Yafi Kowa Kazanta a Duniya, Amou Haji, Ya Rasu Yana Da Shekaru 94 a Duniya. Hoto daga punching.com
Asali: UGC

Haji wanda ya kwashe shekaru babu wanka bai taba aure ba kuma ya mutu a ranar Lahadiwa kauyen Dejgah dake kudancin Fars, IRNA News suka rahoto.

Haji ya dinga gujewa yin wanka sakamakon tsoron kwanciya rashin lafiya da yake yi kamar yadda cibiyar yada labaran ta bayyana.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Amma a karon farko na watanni kadan da suka gabata, mazauna yankin sun tirsashi yin wanka, IRNA suka rahoto.

Wani gajeren bidiyon da aka yi kan rayuwar Amou Haji mai cike da abun mamaki an fitar da shi a shekarar 2013 kamar yadda jaridar Iranian ta bayyana.

Amou Haji: Mutumin da yafi kowa kazanta a duniya, ya yi shekaru 67 babu wanka, yana kwana a rami

A wani labari na daban, Amou Haji tsoho ne mai shekaru 87 wanda ya kwashe shekaru 67 bai yi wanka ba, tabbas hakan yake.

Tsohon dan asalin kasar Iran yana rayuwarsa ne kusa da wani kauye dake kusa da yankin Kermanshah shi kadai kuma ya yi a kalla shekaru 67 babu wanka.

Kamar yadda mazauna yankin suka tabbatar,, Haji a kodayaushe za ka gan shi lullube da toka da datti kuma baya wanka saboda tsoron ruwa da yake yi.

Tsohon mai shekaru 87 ya yadda cewa idan har yayi wanka, toh babu shakka zai iya faduwa mugun ciwo.

Abincin da tsohon yake ci sun hada da rubabben nama da matattun dabbobi. Yana matukar jin dadin cin bushiya da shan tabarsa ta koko, India Times ta ruwaito hakan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel