Sarkin Zazzau Ya Fada Wa Yan Arewa Su Shirya Fuskantar Yunwa A Bana, Ya Bayyana Dalili

Sarkin Zazzau Ya Fada Wa Yan Arewa Su Shirya Fuskantar Yunwa A Bana, Ya Bayyana Dalili

  • Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli, mai martaba sarkin Zazzau ya zaburar da mutanen arewa su yi shirin fuskantar yunwa a bana
  • Sarkin na Zazzau ya ce yan kasar musamman arewa ba su bukatar dan duba ya fada musu cewa za a fuskanci yunwa bana saboda ambaliyar ruwa da yan bindiga sun shafi noma
  • Don haka Sarki Ahmed Nuhu Bamalli ya shawarci al'umma su fara neman wasu hanyoyin da za su taimakawa tattalin arzikinsu a yayin da kuma ake cigaba da addu'an samun saukin lamarin

Kaduna - Mai marataba sarkin zazzaun kuma uba ga hukumar da ke kula da kasuwar duniyar kasa da kasa ta Kaduna (KADCCIMA), Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli, ya yi kira ga arewa ta farka ta magance batun tsananin yunwa, rahoton Daily Trust.

Da ya ke magana a taron KADCCIMA na bada lambar yabo na inganci karo na 3 a Kaduna, sarkin ya ce yankin ba ta bukatar dan duba ya fada mata cewa za ta fuskanci yunwa kuma akwai bukatar da farga domin noma ne abin da yankin ta dogara da shi.

Ambaliya
Ambaliya Ruwa: Ku Shirya Fuskantar Yunwa, Sarkin Zazzau Ya Fada Wa Arewa. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

Ambaliyar ruwa da hare-haren yan bindiga ne sanadin rashin samun isashen abinci a bana

A cewarsa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Batun yunwa yana tafe a bana, baka bukatar dan duba ya fada maka hakan, amma muna addu'a ga Allah da kuma wannan kiran cewa mutane su raba kafa domin idan ka tattare a wuri guda za ka sha mamaki.
"Mu farka daga barcinmu mu ga abin da za mu iya yi kan tattalin arzikin mu wanda shine noma, musamman arewa. Noma ya fuskanci matsala bana saboda abu biyu, ambaliyar ruwa da yan bindiga."

Ya taya wadanda suka samu lambar yabon murna wanda ya ce sun bada gudunmawa sosai ga tattalin arziki a bangarorinsu musamman a arewa.

Ilimin manyan makarantu na da tsada

Sarkin ya kuma yi bayanin cewa ilimin makarantun gaba da sakandare na da tsada a duk duniya yana mai cewa:

"Idan yan Najeriya na son ilimi mai nagarta, sai ka biya. Ba cewa na ke a mutane su biya kudi fiye da kima ba saboda idan ka kwatanta kudin rajista da ake biya a makarantun Najeriya da na kasashen waje, za ka ga cewa muna biyan kasa da yadda ake biya a kasashen waje."

Asali: Legit.ng

Online view pixel