Peter Obi Ya Fi Atiku Alheri, Shi Zan Yi: Cewar Babban Jigon PDP

Peter Obi Ya Fi Atiku Alheri, Shi Zan Yi: Cewar Babban Jigon PDP

  • Da alamun rikicin dake gudana a jam'iyyar PDP zai kaita ta fuskanci matsala a jihar Abia a 2023
  • Gwamnan jihar da kansa, Ikezie Ikpeazu, yana bangare gwamnan Nyesom Wike a rikicin dake gudana
  • Peter Obi dai tsohon dan jam'iyyar PDP ne kuma shi ya yiwa Atiku mataimaki a zaben 2019

Wani cikin yan takaran kujerar gwamnan jihar Abia a zaben fidda gwanin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Sampson Orji, ya bayyana cewa Peter Obi na jam'iyyar LP zai goyi baya a zaben shugaban kasa.

Orji ya bayyana hakan a jawabin da ya fitar ranar Alhamis a Umuahia, birnin jihar Abia, rahoton PremiumTimes.

Ya bayyana cewa ya fifita Peter Obi kan Atiku Abubakar na PDP ne saboda dan takaran na LP ya fi na PDP kwarewa.

Hakazalika yace zai taya Peter Obi yakin neman zabe.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Bayan shafe kwanaki a Faransa, dan takarar PDP Atiku ya dawo Najeriya

Peter Obi
Peter Obi Ya Fi Atiku Alheri, Shi Zan Yi: Cewar Babban Jigon PDP
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa:

"Har gobe ina PDP, amma Obi zai goyi baya, ba dan Inyamuri bane amma saboda abinda yake waklta. Iyali na da abokaina shi zasu zaba."
"Atiku aboki na ne, amma Obi ya fi shi alheri. Sabanin iyawa da akafi Atiku, adalci shine a zabi Obi."
"Me zai hana Atiku ya janye ya goyi bayan obi, ba tare sukayi takara a 2019 ba?
"Kuma gaskiyar magana itace, me muka amfana da PDP cikin shekaru 16 da suka gabata, Titin Aba zuwa Port Harccourt har yanzu bai yiwu ba."

2023: Babban Jigon PDP Ya Ayyana Goyon Bayansa Ga Peter Obi, Ya Koma Jam’iyyar LP

Wani babban jigon jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Lagas, Cif Adesunbo Onitiri, ya sauya sheka zuwa jam’iyyar Labour Party gabannin zaben 2023.

Onitiri ya ce ya bar PDP ne saboda rashin damokradiyyar cikin gida da kuma son marawa takarar shugabancin Peter Obi baya kamar yadda shugaban Afenifere, Pa Ayo Adebanjo ya bukata,

Kara karanta wannan

Peter Obi Ne Mutumin Da Najeriya Ke Bukata: Samuel Ortom Ya Bayyana Goyon Bayansa

Kafin barinsa PDP, Onitiri ya kasance babban dan jam’iyya kuma ya fafata da Sanata Remi Tinubu a zaben neman kujerar majalisar dattawa na 2019.

Dan siyasar ya ce ya bar PDP ne tare da tarin magoya baya, masoya da abokansa a yankin Lagas ta tsakiya don tabbatar da nasarar jam’iyyar LP a babban zabe mai zuwa a jihar Lagas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel