Bidiyon Lokacin da Atiku Ya Dawo Daga Faransa Bayan Wata ’Yar Gajeriyar Tafiya

Bidiyon Lokacin da Atiku Ya Dawo Daga Faransa Bayan Wata ’Yar Gajeriyar Tafiya

  • Bayan shafe kwanaki a kasar waje, bidiyo ya nuna lokacin dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar ya dawo Najeriya
  • Jiga-jigan jam'iyyar PDP na ci gaba da ririta batun takarar Atiku yayin da ake ci gaba da fuskantar zaben 2023
  • Jam'iyyar PDP za ta gudanar taron gangamin kamfen a jihar Edo a karshen makon nan, manyan jiga-jigai za su hallara

Wani bidiyo da muka samo daga jaridar Daily Trust ya nuna lokacin da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya sauka daga jirgi a dawowarsa gida Najeriya.

Rahotanni a baya sun shaida cewa, dan takarar na PDP ya tafi kasar Faransa a wata gajeriyar tafiyar da ba a bayyana dalilin yinta ba.

Atiku ya dawo ne washegarin ranar da jam'iyyar PDP za ta gudanar da taron gangamin na kamfen a jihar Edo, wanda za a yi gobe Asabar 22 ga watan Oktoba.

Kara karanta wannan

Minista Pantami Ya Lashe Lambar Yabon Kirkire-Kirkire na Ilmin Zamani

A tare dashi akwai jiga-jigan jam'iyyar PDP, ciki har da Sanata Dino Melaye, kakakin kamfen din Atiku.

Kalli bidiyon:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Mun Daina Zunubi Domin Dan Takaranmu Atiku Ya Samu Nasara, Inji Dino Melaye

A bangare guda, mai magana da yawun kwamitin kamfen din jam'iyyar PDP a gangamin zaben shugaban kasa na 2023, Sanata Dino Melaye ya bayyana cewa, wasu mambobin majalisar sun daina aikata zunubi saboda nemawa Atiku nasara a zabe mai zuwa.

Melaye ya bayyana hakan ne a wani taro da mambobin jam'iyyar PDP a jihar Kaduna, inda gangamin kamfen din jam'iyyar ya gudana, Daily Trust ta ruwaito.

Ya karanto wasu ayoyin Al-Qur'ani tare da cewa, wasu jiga-jigan PDP sun kame daga aikata zunubu ne domin kwadayin Allah ya amsa addu'arsu idan suka roke shi game da nasarar Atiku.

Jam’iyyar PDP Za Ta Gudanar da Taron Gangamin Kamfen Na Takarar Shugaban Kasa a Jihar Edo Ranar Asabar

Kara karanta wannan

Pantami, Wike, Jonathan: Hotunan Mutum 44 Da Shugaba Buhari Ya Karrama Yau

A wani labarin kuma, tawagar kamfen din tallata dan takarar shugaban kasan PDP za ta karkata zuwa jihar Edo a ranar Asabar 22 ga watan Oktoba domin gudanar da gangamin lasawa 'yan Najeriya alkawuran Atiku.

Rahoton da muka samo daga jaridar Punch ya bayyana cewa, ana sa ran duk wasu jiga-jigan PDP za su hallara a filin taro da misalin karfe 10 na safiyar ranar.

Hakazalika, rahoton ya ce, dukkan gwamnonin da aka zaba a karkashin inuwar PDP za su hallara a wannan taro mai girma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel