2023: Babban Jigon PDP Ya Ayyana Goyon Bayansa Ga Peter Obi, Ya Koma Jam’iyyar LP

2023: Babban Jigon PDP Ya Ayyana Goyon Bayansa Ga Peter Obi, Ya Koma Jam’iyyar LP

  • Babban jam’iyyar PDP mai adawa a kasar ta rasa wani babban jigonta a jihar Lagas, Cif Adesunbo Onitiri, ya koma Labour Party
  • Onitiri ya ce ya koma jam’iyyar LP ne don goyon bayan takarar shugabancin Peter Obi
  • Tsohon jihon na PDP ya kuma bayyana cewa rashin damokradiyya a tsohuwar jam’iyyarsa ne yasa shi komawa bayan Obi

LagosWani babban jigon jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Lagas, Cif Adesunbo Onitiri, ya sauya sheka zuwa jam’iyyar Labour Party gabannin zaben 2023.

Onitiri ya ce ya bar PDP ne saboda rashin damokradiyyar cikin gida da kuma son marawa takarar shugabancin Peter Obi baya kamar yadda shugaban Afenifere, Pa Ayo Adebanjo ya bukata, Nigerian Tribune ta rahoto.

Peter Obi daAdesunbo Onitiri
2023: Babban Jigon PDP Ya Ayyana Goyon Bayansa Ga Peter Obi, Ya Koma Jam’iyyar LP Hoto: @PeterObi, @onitiri4senate
Asali: Twitter

Kafin barinsa PDP, Onitiri ya kasance babban dan jam’iyya kuma ya fafata da Sanata Remi Tinubu a zaben neman kujerar majalisar dattawa na 2019.

Kara karanta wannan

Wasu Shugabannin PDP na Neman Tada Rikici, Sun ce An Ware Su a Yakin Zaben Atiku

Dan siyasar ya ce ya bar PDP ne tare da tarin magoya baya, masoya da abokansa a yankin Lagas ta tsakiya don tabbatar da nasarar jam’iyyar LP a babban zabe mai zuwa a jihar Lagas.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon dan PDPn ya kuma bukaci matasan Najeriya da su kwato kasarsu daga mulkin kama karya da tsoffin yan siyasa suka shafe tsawon shekaru 62 suna yi.

Ya kuma bayyana cewa zabe mai zuwa yana da muhimmanci kuma shine zai tabbatar da ci gaba da wanzuwar kasar.

Onitiri ya bukaci yan Najeriya da kada su siyar da kuri’unsu sannan cewa su yi zabe cikin hikima, rahoton The Guardian.

Ya ce:

“Najeriya na tsananin rashin lafiya da za a barta a hannun tsoffi, marasa kishi, masu kabilanci kuma yan siyasa da ta kare masu don su yi jagoranci.”

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Atiku Ya Shilla Turai Ana Tsaka da Gangamin Yakin Neman Zabe

Ya kara da cewar yan Najeriya na bukatar mutum mai kuzari da shugaba mai hangen nesa don gyara matsalolin gidan.

2023: Da Ace Ni Ba Dan PDP Bane, Da Zan Taimaki Peter Obi Ya Zama Shugaban Kasa, Gwamnan Arewa

A wani labarin, Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue ya bayyana cewa ba don shi dan PDP bane da babu abun da zai hana shi aiki don ganin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party (LP), Peter Obi, ya lashe zabe mai zuwa.

Ortom ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, 19 ga watan Oktoba, yayin da ya karbi bakuncin tsohon gwamnan na jihar Ana,bra a gidansa da ke Abuja, Channels TV ta rahoto.

Ortom ya ce ba lallai ne ace Obi na da abubuwan bukata ba, amma idan Allah ya zartar da hukunci, babu wanda ya isa ya hana shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel