Jami'ar ABU Ta Sanar da Ranar Komawa Aiki Bayan ASUU Ta Janye Yajin Aiki

Jami'ar ABU Ta Sanar da Ranar Komawa Aiki Bayan ASUU Ta Janye Yajin Aiki

  • Jami'ar Ahmadu Bello University dake Zariya a jihar Kaduna ta sanar da ranar buɗe makaranta bayan janye yajin aikin ASUU
  • A wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai na ABU, Malam Auwal Umar, ya fitar yau Laraba yace za'a koma aiki ranar 24 ga watan Oktoba
  • Yace majalisar gudanarwar jami'ar a wani taron gaggawa ta amince da garambuwal ga Kalandar karatun 2021/2022

Zaria, Kaduna - Jami'ar Ahmadu Bello (ABU) Zariya dake jihar Kaduna ta sanar da ranar 24 ga watan Oktoba, 2022 a matsayin ranar komawa harkokin karatu gadan-gadan bayan janye yajin aikin ASUU.

Daraktan harkokin yada labarai na jami'ar ABU, Malam Auwal Umar, shi ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba a Zariya, kamar yadda PM News ta ruwaito.

Ahmadu Bello University Zariya.
Jami'ar ABU Ta Sanar da Ranar Komawa Aiki Bayan ASUU Ta Janye Yajin Aiki Hoto: pmnews
Asali: Twitter

Yace za'a koma aji ne biyo bayan janye yajin aikin kungiyar Malaman jami'o'i ta kasa wanda ya shafe watanni Takwas.

Kara karanta wannan

Tsohon Ɗan Takarar Shugaban Kasa a APC Ya Jingine Tinubu, Ya Faɗi Wanda Yake So Ya Gaji Buhari a 2023

A ruwayar The Nation, Malam Umar yace majalisar gudanarwan jami'ar ce ta amince da ranar komawa makarantar a wani taron gaggawa karo na 516 da ta gudanar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kuma kara da cewa majalisar ta amince da sake duba wa tare da yi wa Kalendar karatun shekarar 2021/2022 garambawul.

A cewarsa, kalandar da majalisar ta amince da ita a taronta karo 513 wanda ya gudana ranar 25 ga watan Nuwamba, 2021 tana bukatar gyara sakamakon yajin aikin da aka tafi wanda aka janye makon da ya shude.

Ƙungiyar ASUU ta shiga yajin aiki ne tun a watan Fabrairun wannan shekarar 2022 kan wasu bukatu da suka nemi gwamnatin tarayya ta cika musu.

Bayan kai ruwa rana, kungiyar ta janye yajin aikin ranar Jumu'a, inda tace ta yi haka ne domin biyayya ga umarnin Kotu.

Kara karanta wannan

Kamfen 2023: 'Yan A Mutun APC Na Bin Gida-gida Don Tallata Dan Takararsu Bola Tinubu A Wata Jahar Arewa

Babban Abinda ya sa muka janye yajin aiki - ASUU

A wani labarin kuma Kungiyar ASUU ta bayyana muhimmin abun da ta kalla har ta janye yajin aikin da yake yi

Shugaban kungiyar ASUU ta malaman jami’a, Emmanuel Osodeke yace hukuncin kotu ne babban abin da ya tursasa masu komawa bakin aiki.

Farfesa Emmanuel Osodeke ya kara da cewa malamai sun janye yajin-aikin da su ke yi ne saboda Alkali ya umarci su bude makarantu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel