Jirgin Ruwa Ya Nitse da Fasinjoji Sama da 50, Rayuka 33 Sun Salwanta a Niger

Jirgin Ruwa Ya Nitse da Fasinjoji Sama da 50, Rayuka 33 Sun Salwanta a Niger

  • A kalla rayuka 33 aka saka lace an rasa bayan hatsarin jirgin ruwa ya ritsa da sama da fasinjoji 50 dake jirgin ruwa a kogin Kaduna a jihar Neja
  • Kamar yadda aka gano, fasinjojin akasarinsu ‘yan kasuwa ne dake dawowa bayan sun ci kasuwar Danchitagi kuma miliyoyin naira sun salwanta
  • Hukumar agajin gaggawa ta sanar da cewa an ceto mutane 17 daga cikin fasinjojin amma dadewar da sauran suka yi a ruwan ne yasa aka sakankance sun mutu

Niger - Akalla mutum 33 da suka hada da mata da yara ne suka mutu bayan wani jirgin ruwa dauke da fasinjoji fiye da 50 ya kife a kogin Kaduna da ke jihar Neja.

Daily Trust ta rahoto cewa jirgin ruwan ya kife ne tsakanin kauyen Danchitagi da ke karamar hukumar Lavun da Gbara da ke karamar hukumar Mokwa a jihar Neja a daren ranar Juma’a.

Kara karanta wannan

Abin da Ya Sa Gwamnatin Tarayya Ta Saki ‘Yan Boko Haram 100 Daga Kurkuku a Boye

Hatsarin jirgin ruwa
Jirgin Ruwa Ya Nitse da Fasinjoji Sama da 50, Rayuka 33 Sun Salwanta a Niger. Hoto daga Sahara Reporters
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Majiyoyi sun bayyana cewa wasu daga cikin fasinjojin yan kasuwa ne da ke hanyarsu ta dawowa daga kasuwar mako da ke a Danchitagi yayin da sauran ke hanyarsu ta komawa gida bayan sun halarci wani daurin aure a garuruwan da ke makwabtaka.

An kuma rahoto cewa anyi asarar dukiya na miliyoyin naira a hatsarin.

Mazauna kauyen sun bayyana cewa zuwa yanzu an ceto mutum 17 daga cikin fiye da 50 da ke jirgin ruwan yayin da ake ci gaba da aikin ceto.

Daya daga cikin masu shiga ruwan yace:

“A yanzu haka, daga cikin mutum fiye da 50 da ke jirgin ruwan, mutum 17 kacal aka ceto da ransu. Muna sa ran sauran basa raye saboda sun shafe tsawon awanni a cikin ruwan. Ruwan na da zurfi sosai a yanzu saboda ruwan sama. Har yanzu muna iya bakin kokarinmu na neman sauran mutanen, amma babu tabbacin zasu rayu.”

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: An kama wasu 'yan Kamaru da kokon kan mutum a Arewacin Najeriya

Daily Trust ta tattaro cewa lamarin ya afku ne sakamakon ruwan sama da aka zuba kamar da bakin kwarya, da kuma iska mai karfi.

Yawancin wadanda abun ya ritsa dasu sun fito ne daga garuruwan da ke bakin ruwa na Muregi, Gbara, Gazhe, Tadima da sauransu.

An kwashi wasu daga cikin mutanen da aka ceto zuwa asibitin Gbara domin samun kulawar likita.

Darakta Janar na hukumar bayar da agajin gaggawa na jihar Neja, Ahmed Ibrahim Inga, ya tabbatar da faruwar lamarin amma yace ba zai iya bayar da cikakken bayani kan adadin mutanen da suka mutu ba.

Yace hukumar bayar da agajin gaggawa sun shiga aikin ceto da nufin ceto sauran mutane.

Hakimin Gbara, Alhaji Mohammed Saba, wanda shima ya tabbatar da lamarin, yace akalla mutum 60 ne ke a cikin jirgin ruwan.

Hatsarin jirgin ruwa a Kano: Adadin mutanen da suka mutu a hatsarin ya ƙaru, Jami'ai na cigaba da aiki

Kara karanta wannan

Ana Zargin Sojoji Da Mamaye Wani Yanki A Enugu, Sun Kone Gidaje Da Dama

A wani labari na daban, adadin mutanen da suka mutu a hatsarin jirgin ruwa wanda ya auku a jihar Kano ranar Talata ya ƙaru zuwa 29.

Tun a ranar da lamarin yafaru aka samu nasarar fito da gawarwakin mutum 20 cikin su harda na ɗaliban Isalmiyya.

Lokacin da jaridar Dailytrust ta ziyarci Bagwai, wurin da lamarin ya faru, wani babban jami'in hukumar kwana-kwana, Saminu Yusuf Abdullahi, ya tabbatar da cewa an sake ciro gawar mutum 9.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel