Hatsarin jirgin ruwa a Kano: Adadin mutanen da suka mutu a hatsarin ya ƙaru, Jami'ai na cigaba da aiki

Hatsarin jirgin ruwa a Kano: Adadin mutanen da suka mutu a hatsarin ya ƙaru, Jami'ai na cigaba da aiki

  • Rahotanni sun bayyana cewa an sake tsamo gawar mutum 9 daga cikin waɗan da hatsarin jirgin ruwa ya rutsa da su a Kano
  • Zuwa yanzun adadin waɗan da suka mutu ya kai jimullan mutum 29, cikinsu harda ɗaliban islamiyya dake hanyar zuwa wurin Maulidi
  • Gwamna Ganduje na jihar Kano ya yi kira ga masu jiragen ruwa su daina cika wa abun hawansu kaya da yawa

Kano - Adadin mutanen da suka mutu a hatsarin jirgin ruwa wanda ya auku a jihar Kano ranar Talata ya ƙaru zuwa 29.

Tun a ranar da lamarin yafaru aka samu nasarar fito da gawarwakin mutum 20 cikin su harda na ɗaliban Isalmiyya.

Lokacin da jaridar Dailytrust ta ziyarci Bagwai, wurin da lamarin ya faru, wani babban jami'in hukumar kwana-kwana, Saminu Yusuf Abdullahi, ya tabbatar da cewa an sake ciro gawar mutum 9.

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum ya ɗauki nauyin marayu 500 na yan sakai da suka rasa ransu a yaƙi da Boko Haram

Hatsarin ruwa
Hatsarin jirgin ruwa a Kano: Adadin mutanen da suka mutu a hatsarin ya ƙaru, Jami'ai na cigaba da aiki Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Jirgin ruwan ya nutse ne yayin da ya ɗakko fasinjoji, waɗan da mafi yawan su ɗaliban makarantar Madinatu Islamiyya ne daga kauyen Badau, zuwa Bagwai domin halartan bikin Maulidi.

A halin yanzun, dukkan gawarwakin da aka tsamo daga cikin ruwan, an yi musu jana'iza kamar yadda addinin musulunci ya tanadar.

Rahotanni sun bayyana cewa daga waɗan da hatsarin ya rutsa da su akwai wasu mata 8, waɗanda suka zo ziyara daga Naibawa dake cikin kwaryan birnin Kano.

An gano gawarwakin shida daga cikin matan guda takwas, yayin har yanzun ba'a ga sauran biyun ba, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Ganduje ya yi jimami

Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana hatsarin a matsayin wata masifa da ta auku a jihar.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Allah ya yiwa Wazirin masarautar Hadejia rasuwa

Ya kuma yi addu'a ga mamatan, Allah ya gafarta musu kurakuransu, yayin da ya yi fatan samun lafiya ga waɗan da ke kwance a Asibiti.

Gwamnan ya gargaɗi masu jiragen ruwa da su guje wa cika wa abun hawansu kaya da yawa, a sanarwan da sakataren yaɗa labaran gwamnan, Abba Anwar, ya fitar.

"Ya kamata ku sani cewa zaku samu riba ko da baku cika wa abin hawan ku kaya ba.'

A wani labarin na daban kuma Ganduje ya yi magana kan daliban Islamiyya 20 da suka mutu a hatsarin jirgin ruwa a Kano

Ganduje ya roki matukan jirgin ruwa su daina cika wa abun hawan su kaya har ya fi ƙarfinsa, domin rayuwar mutane ce a gaba.

Ya kuma yi addu'ar samun rahamar ubangiji ga waɗan da suka mutu, tare da fatan samun lafiya ga waɗan da ke kwance a Asibiti.

Asali: Legit.ng

Online view pixel