Katsina: Shugabannin ‘Yan Bindiga 7 Sun Yada Makamai, Suna Neman Sulhu da Gwamna Masari

Katsina: Shugabannin ‘Yan Bindiga 7 Sun Yada Makamai, Suna Neman Sulhu da Gwamna Masari

  • Hadimin Gwamna Masari na jihar Katsina kan lamurran tsaro, Ibrahim Ahmad Katsina ya bayyana cewa kwamandojin ‘yan bindiga 7 a jihar ne ke neman sulhu
  • Katsina ya sanar da cewa manya kwamandojin sun ajiye makamai tare da tunkarar gwamnatin jihar domin yin sasanci mai dorewa da kawo zaman lafiya
  • Ya sanar da cewa duk rikicin nan na ‘yan bindiga ya kusa zuwa karshe kuma tuni suka fara tallafawa matan da aka halaka mazansu da ayyuka, sana’ar yi da kasuwanci

Katsina - Shugabannin ‘yan bindiga bakwai a jihar Katsina sun ajiye makamansu tare da neman gwamnatin jihar domin yin sasanci mai dorewa.

Taswirar Katsina
Katsina: Shugabannin ‘Yan Bindiga 7 Sun Yada Makamai, Suna Neman Sulhu da Gwamna Masari. Hoto daga TheCable.ng
Asali: UGC

Mai bada shawara na musamman ga gwamnan jihar kan lamurran tsaro, Ibrahim Ahmad Katsna ya bayyana hakan ga gidan Talabijin na Channels a ranar Juma’a.

Kara karanta wannan

Gwamnoni 2 za su ba 'yan banga AK-47, rundunar soji ta yi martani mai zafi

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya bayyana cewa shugabannin ‘yan bindigan sun gano abinda gobe zata haifar musu don hakan suka tunkari gwamnatin jihar domin tabbatar da samun cigaba.

Kamar yadda Ahmad Katsina ya bayyana, kokarin gwamnatin jihar kan ‘yan jihar tuni ya fara kawo sakamako mai kyau ganin yadda farmakin ‘yan bindiga ya ragu.

Ya sakankance cewa duk wasu miyagun ayyuka da suka hada da ‘yan bindiga, garkuwa da mutane da sauran laifuka sun kusa zuwa karshe sakamakon kokari na hadin guiwa da aka samu tsakanin ‘yan jihar da gwamnati wurin taimakawa jami’an tsaro.

Hakazalika, ya tuna yadda gwamnatin jihar a baya-bayan nan ta horar da ‘yan sa kai 1,100 wadanda zasu dinga taimakawa al’umma, kokarin da ya zama tamkar sako ga ‘yan bindigan don su rungumi zaman lafiya.

Hadimin Gwamnan yayi bayanin cewa gwamnatin jihar ta kaddamar da wani babban kwamiti karkashin jagorancin mataimakin Gwamnan jihar Mannir Yakubu, domin dauko kididdigar wadanda rikicin ‘yan bindigan ya ritsa dasu.

Kara karanta wannan

Sabon salo: Gwamnan PDP ya nada masu bashi shawara kan harkar siyasa mutum 50,000

An yi hakan ne domin tabbatar da cewa ba a nuna halin ko in kula ga wadanda lamarin ya shafa ba kuma don gujewa wani rikici bayan harin ‘yan bindigan ya zo karshe.

“Muna amfani da saukakan dabarun sanin halayyar ‘dan Adam ne wurin shawo kan abinda yara zasu fahimta a wuraren da rikicin ‘yan bindigan ya shafa. Wannan kuwa mun yi shi ne saboda gane cewa yaran da lamarin ya shafa zasu so daukar fansa. Don haka ne muke tallafa musu.
“Za mu samar da ayyukan yi ga matan da aka kashe mazansu, sana’o’i da kasuwanci kuma za mu kai ‘ya’yansu makaranta. Wannan kokarin kuwa yana samar da abinda ake so.”

- Katsina ya jaddada.

Hotunan Buhari Yayin da ya Ziyarci Ragowar Fasinjojo 23 na Jirgin Kasa da Boko Haram Suka Saki

A wani labari na daban, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis ya hana da fasinjoji 23 na jirgin kasa da suka samu ‘yanci a ranar Laraba a asibitin makarantar horar da hafsoshin soji dake Kaduna.

Kara karanta wannan

Zan Tabbatarwa 'Yan Najeriya Tsaro Kafin Na Mika Mulki, Buhari Ya jaddada

Fadar shugaban kasa ta tabbatar da hakan a wata wallafa da tayi a Twitter a ranar Alhamis.

An sako sauran fasinjojin 23 da aka sace a jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna a ranar Laraba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel