Nnamdi Kanu: Majalisar Tsaron Najeriya Ta Yi Karin Haske Kan Shugaban IPOB, Ta Bayyana Mataki Na Gaba
- An sallami, shugaban haramtaciyyar kungiyar masu neman kafa kasar Biafra, IPOB, Nnamdi Kanu ne amma ta wanke shi daga dukkan zargi aka yi ba
- Wannan shine matakin Majalisar Taro na Kasa ta Najeriya a ranar Juma'a 14 ga watan Oktoba, kwana guda bayan kotun daukaka kara ta kore zargin ta'addanci da ake yi wa Kanu
- Ministan Harkokin Yan Sanda, Maigari Dingyadi, ya ce gwamnatin tarayya tana duba mataki na gaba da za ta dauka kan lamarin
FCT Abuja - Majalisar Tsaro na Kasa a Najeriya ta yi karin haskewa kan matsayin Gwamnatin Tarayya dangane da shari'ar shugaban haramtaciyyar kungiyar masu neman kafa kasar Biafra, IPOB, Nnamdi Kanu.
Ta ce har yanzu Kanu na da shari'ar da zai amsa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Kotun daukaka kara a Abuja a ranar Alhamis, ta yi soke tuhumar ta'addanci da ake yi wa Kanu, abin da ya janyo cece-kuce a bangarori da yawa na kasar.
An fassara hakan na nufin za a sako shi daga inda ya ke tsare.
Amma, Antoni Janar na kasa kuma ministan shari'ar, Abubakar Malami, ya ce ba a wanke Kanu ba saboda akwai wasu tuhume-tuhumen da ake masa.
Nnamadi Kanu: Majalisar Tsaro na Kasa ta yarda da matsayar Malami
Bisa wannan tsarin, ita ma Majalisar Tsaro na kasa, wacce Shugaba Muhammadu Buhari ke yi wa jagoranci, ta ce gwamnati na duba mataki na gaba da za ta dauka.
Da ya ke yi manema labarai jawabi bayan taron majalisar, Ministan harkokin yan sanda, Maigari Dingyadi, tare da ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, da babban hafsan tsaro, Janar Lucky Irabor, sun ce za a cimma matsaya kan abin da zai faru da Kanu cikin yan kwanaki masu zuwa.
Dingyadi ya ce:
"Kazalika, an yi magana kan Kanu kuma an yi wa majalisar jawabi kan inda aka tsaya kuma an lura an sallami Kanu amma ba a wanke shi daga tuhume-tuhume ba.
"Don haka, gwamnati na duba matakin da ya dace ta dauka kan batun kuma za ta sanar da yan Najeriya matsayar ta kan lamarin a nan gaba."
Ya majalisar kawai ta tatauna hukuncin kotun daukaka karar ne yana mai cewa za a iya tattaunawa kan irin wannan batutuwan tunda yanzu ba a gaban kotu abin ya ke ba.
Kotun Daukaka Kara Ta Sallami Shugaban IPOB, Nnamdi Kanu, Ta Kallubalanci Hukuncin Babban Kotu
Tunda farko, kotun daukaka kara da ke zamanta a birnin tarayya Abuja ta sallami shugaban haramtaciyyar kungiyar Indigenous People of Biafra, IPOB, Nnamdi Kanu, Channels Television ta rahoto.
Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta gurfanar da Kanu ne a babban kotun tarayya da ke Abuja kan tuhume-tuhume 15 masu alaka da cin amanar kasa da ta'addanci da ta ke zargin ya aikata yayin fafutikan neman ballewa daga Najeriya.
Asali: Legit.ng