Matashi Mara Kafafu da Hannaye Yana Sarrafa TikTok a Bidiyo da Lebensa, Ya Ba Jama’a Mamaki

Matashi Mara Kafafu da Hannaye Yana Sarrafa TikTok a Bidiyo da Lebensa, Ya Ba Jama’a Mamaki

  • Wani mutum mai nakasa mai suna Gabe Adams-Wheatley ya kwatanta wani abun mamaki na yadda yake amfani da lebensa
  • Gabe wanda aka haifa babu kafafu balle hannaye yana amfani da TikTok da lebensa na sama kuma cike da hanzari
  • Mutumin ya nuna kwazonsa a wani bidiyo wanda ya matukar birge ‘yan soshiyal midiya yayin da wasu kuwa saurinsa ya dauki hankalinsu

Gabe Adams-Wheatley wani mutum ne mai nakasa wanda ya bai wa jama’a mamaki da yadda yake amfani da labbansa.

Ya bayyana yadda yake amfani da labbansa a shafinsa na TikTok domin martani ga jama’a da suke tunanin ba zai iya martani kan tsokacinsu ba na soshiyal midiya saboda rashin hannayensa.

Physically Challenged
Matashi Mara Kafafu da Hannaye Yana Sarrafa TikTok a Bidiyo Ya Ba Jama’a Mamaki. Hoto daga TikTok/@gabeadams
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Wani Matashi Ɗan Najeriya Na Shirin Wuf da Wata Baturiya Da Suka Hadu A TikTok

A yayin amfani da lebensa na sama cike da sauri, Gabe ya bude manhajar tare da yin tsokaci ba tare da taimakon kowa ba.

A yayin martani ga tsokacin da aka yi a kasan bidiyon, ya bayyana yadda fuskar wayarsa take bayan yayi amfani da lebensa wurin budeta.

Yan soshiyal midiya sun yi martani

Phea Plumlee391 tace:

“Ina alfahari da kai, wannan abu yayi kyau.”

Case Duarte yace:

“Wannan abu da birgewa yake! Ya idanunka suke? Da kyar nake iya rubutu da kumbuna na.”

Allana S tace:

“A gaskiya kana da sauri, kana rubutu da sauri fiye da ni kuma ina da yatsu.”

Tegan Vincent-Cooke yace:

“A gaskiya wannan abun birgewa ne.”

BillyBob tace:

“Idan fa mutum ya dauke ka tare da arcewa.”

Bayan Shekaru 47 da Barin Gida Yana Matashi, Ya Dawo a Tsoho, Babu Arzikin da Yaje Nema

A wani labari na daban, Bidiyon tsohon da ya dawo gida daga kasar waje bayan kwashe shekaru 47 ya bai wa jama’a mamaki.

Kara karanta wannan

Bidiyon malamin makarantan da ya tafi banki da 'Ghana Must Go' don karbo albashinsa

A bidiyon, mutumin ya tsufa kuma kwatsam ya tuna gida tare da dawowa inda ya bai wa ahalinsa mamaki.

Labarin mutumin mai suna Peter Shitanda an wallafa shi ne a YouTube a tashar Afrimax ta Turanci kuma ta janyo cece-kuce.

Peter ‘dan asalin kasar Kenya ne kuma ya bar kauyensu inda ya koma kasar Tanzania tare da fatan zai yi arziki mai yawa.

Ya fara zama a Nairobi kafin ya koma Tanzania inda yayi aiki kusa da tsaunin Kilimanjaro.

Asali: Legit.ng

Online view pixel