Wani Matashi Ɗan Najeriya Na Shirin Wuf da Wata Baturiya Da Suka Hadu A TikTok

Wani Matashi Ɗan Najeriya Na Shirin Wuf da Wata Baturiya Da Suka Hadu A TikTok

  • Wani matashin ɗan Najeriya, Gideon Raphael, ya bayyana wa duniya baturiyar da yake soyayya da ita a shafinsa na intanet
  • Matashin dai ya shafe kusan watanni uku yana sharɓar soyayyar da wannan baturiya
  • Sannan ya saka wani bidiyo da ke nuna yadda ya tarbe ta a tashar jirgin sama a lokacin da ta iso Najeriya

Wani matashi mai suna Gideon Raphael da ke soyayya da wata baturiya ya yi nasarar haɗuwa da ita a zahiri.

Masoyan dai sun haɗu ne ta kafar sada zumunta, inda Raphael ɗin ya bayyana cewa sun sha soyayya ne na tsawon watanni uku kafin haɗuwar tasu.

Sannan Raphael ya saki wani bidiyo a TikTok da ke nuna yadda ya yi mata maraba a yayin da ta fito daga jirgin sama.

Masoyan, a yayin da suka ga juna a zahiri a karon farko, sun cika da farin ciki tare da rungumar juna, inda ya jefa hannunsa a wuyanta tare da yi mata jagora.

Kara karanta wannan

Abun Tausayi: An Gano Wani Bawan Allah Tsirara da Aka Kulle Tsawon Shekara 20 a Kaduna

TikTOk
Wani Matashi Ɗan Najeriya Na Shirin Wuf da Wata Baturiya Da Suka Hadu A Facebook
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mutane da yawa dai sun bayyana ra'ayoyinsu a kan wannan al'amari a kafafen sada zumunta.

Ga abinda wasu ke cewa:

Mai suna MORE_SAY IK'ASIAN cewa ya yi:

"mata ko kaka"

Sannan Deborah Ayiku said:

"Yanzu ba sa bari a mazanmu su yaudare su (matan turawa)...Aure kawai".

Shi kuwa Klimop,

"mutumina kar ka yi wasa da wannan dama da Ubangiji ya ba ka."

A cewar Richie_ralph,

"Wannan duk zancen banza ne, ba ka san abin da ake nufi da soyayyar gaskiya ba ne. Amma ina taya ka murna.

Ko yaya kuke kallon wannan al'amari na Wuf da ake cigaba da fuskanta daga matan Turawa kuma me ya sa mazanmu na Najeriya ke rawar jikin auren irin waɗannan Turawa?

Asali: Legit.ng

Online view pixel