Bayan Shekaru 47 da Barin Gida Yana Matashi, Ya Dawo a Tsoho, Babu Arzikin da Yaje Nema

Bayan Shekaru 47 da Barin Gida Yana Matashi, Ya Dawo a Tsoho, Babu Arzikin da Yaje Nema

  • Tsohon da ya kwashe shekaru 47 a kasar waje ba tare da ya waiwayo iyalansa ba ya dawo gida amma cike da abun mamaki
  • Peter Shitanda ya fice daga kasarsa yayin da yake matashi domin neman arziki amma bai samu ba kuma ya kasa dawowa gida da wuri
  • A lokacin da ya kama hanya ya dawo gida cikin iyalansa, basu gane shi ba saboda ya tsufa kuma ya canza ba kadan ba

Bidiyon tsohon da ya dawo gida daga kasar waje bayan kwashe shekaru 47 ya bai wa jama’a mamaki.

A bidiyon, mutumin ya tsufa kuma kwatsam ya tuna gida tare da dawowa inda ya bai wa ahalinsa mamaki.

Old Man
Bayan Shekaru 47 da Barin Gida Yana Matashi, Ya Dawo a Tsoho, Babu Arzikin da Yaje Nema. Hoto daga YouTube/Afrimax
Asali: UGC

Labarin mutumin mai suna Peter Shitanda an wallafa shi ne a YouTube a tashar Afrimax ta Turanci kuma ta janyo cece-kuce.

Kara karanta wannan

Rikici: Tashin hankali yayin da kanin miji ya kwace wa dan uwansa mata mai 'ya'ya 7

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Peter ‘dan asalin kasar Kenya ne kuma ya bar kauyensu inda ya koma kasar Tanzania tare da fatan zai yi arziki mai yawa.

Ya fara zama a Nairobi kafin ya koma Tanzania inda yayi aiki kusa da tsaunin Kilimanjaro.

A yayin da Peter ya kasa samun arzikin da ya tafi nema, ya kasa komawa gida.

Iyalansa sun dinga jiransa amma kamar an shuka dusa, lamarin da yasa matansa suka kara aure.

Ya’yan Peter sun kasa gane shi

Daya daga cikin ‘ya’yansa maza wanda shekarunsa hudu yayin da ya bar gida, ya kasa gane shi a lokacin da ya dawo da tsufansa.

Abun mamaki, tsohon ya koma gida da wasu ‘yan jakunkuna ba tare da arzikin da zai nuna yace ya samu ba a cikin shekarun.

Ma’abota amfani da YouTube sun yi martani

Kara karanta wannan

Tsohon Gwamnan Arewa Da Buhari Ya Yi Wa Afuwa Ya Fadi Yadda Za'a Kawo Karshen Cin Hanci da Rashawa a Najeriya

Bless Bunny tace:

“Ban fahimci me yasa ya tsaya can ba dogon lokaci ba, tabbas yana da labarai da zai bai wa iyalansa.”

Rosebelle Waihenya tayi tsokaci da:

“Wasu mutanen mugaye ne, mahaifina ma haka aka taso da shi. Mahaifinsa sai yayi tafiyarsa na shekaru tara kuma ya dawo hannu na dukan cinya. Ya kara haihuwar wasu ‘ya’yan sannan ya kara yin gaba.
“Wannan mutumin bashi da kudin komawa gida amma yana da kudin kara aure, bai damu ba kan ci da shan ‘ya’yansa amma yanzu yana bukatar mai kula da shi duk da ya dawo hannu na dukan cinya.”

Abun Mamaki: Bidiyon Matar da ta Haifa Yara 11 dukkansu Makafi, da Yadda Take Kula dasu

A wani labari na daban, bidiyon Agnes Nespondi, wata mata ‘yar kasar Kenya wacce ta haifa yara 11 duk makafi ya dauka hankali a YouTube.

Bidiyon mai tsayin mintuna 8 da sakan 10 an wallafa shi ne a a Afrimax na Turanci kuma ya bayyana mahaifiyar tana kokarin kula da yaranta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel