Bidiyon Mata Mai Juna Biyu Dake Aikin Gini Ya Ba Jama'ar Intanet Tausayi

Bidiyon Mata Mai Juna Biyu Dake Aikin Gini Ya Ba Jama'ar Intanet Tausayi

  • Wani bidiyo mai taba zuciya ya nuna lokacin da wasu mata biyu ke aikin leburanci a jihar Enugu dake Kudancin Najeriya
  • A bidiyon da Lucky Udu ya yada na matan; daya mai juna, daya kuma shayarwa, an ga lokacin da suke aikin gini, suna daukar nauyi
  • Daya daga ciki, mai cikin wata 5 ta ce mijinta bai da abin yi don haka dole ta yi aiki don tabbatar da ta rike gida

Wani bidiyo mai taba zuciya ya nuna lokacin da wata mata mai juna biyu dake aikin gini, lamarin da ya jawo martanin jama'a a kafar TikTok.

Ba ita kadai ba, an kuma ga wata mata dake shayarwa a wurin aikin ginin, duk kuma sun zo ne domin neman kudin rike iyalansu.

Mace mai ciki dake aikin gini
Bidiyon Mata Mai Juna Biyu Dake Aikin Gini Ya Ba Jama'ar Intanet Tausayi | Hoto: TikTok/Lucky Udu
Asali: UGC

A bidiyon da Lucky Udu ya yada, an ga matan dauke da kwangiri makare da kwababbar kasa a lokacin da ake aikin gini.

Kara karanta wannan

An Rasa Ran Mutum 1 a Farmakin da ‘Yan Bindiga Suka kai Maitama Dake Abuja

Matar mai shayarwa ta tsaya a tsakar rana domin ta ba dan da take goyo mama.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Lucky Udu ya ce, ya gano matan ne a wani wurin da ake aikin gini a jihar Enugu. Matar mai ciki ta yi korafin cewa, tana wannan aikin wahala ne tun bayan da mijinta ya rasa aikin yi.

Kalli bidyon:

Martanin jama'a

@Teddy Alex425 yace:

"Gwamnatin Najeriya ta gaza a idonmu."

@LEO yace:

"Lamari dai bai yi dadi ba."

@kcee yace:

"Lucky a ina cikin jihar Enugu kenan ka ga wannan???"

@Mimidred Signature yace:

"Allah ka kawo wadannan dauki."

@Toke_yoruba yace:

"A haka kuma kuke zagin Teni don ta ki shan hannu da Buhari!"

@user8661266823171 yace:

"Kuma a haka mutanen Enugu za su zabi Atiku ko Tinubu, don Allah ku zabi Peter Obi."

Kara karanta wannan

Bidiyon malamin makarantan da ya tafi banki da 'Ghana Must Go' don karbo albashinsa

@user7991735996305 yace:

"Allah zai turo mana wanda zai taimake a wannan kasar da ake kira Najeriya."

@user3480654445658 tace:

"'Yan uwana mata na fafutukar ciyar da 'ya'ya, Allah ya biya ku da gidan aljanna.

@davekoko749 yace:

"Mutumin da ya ba mata mai ci aikin shine mugu."

Budurwa Ta Kai Kaninta Jami'a Cotonou, Ta Yi Masa Rijistar N210k

A wani labarin, bidiyon wata budurwa 'yar Najeriya da ta yiwa kaninta rajistar makaranta a jami'ar Cotonou ya yadu a intanet, jama'a da dama sun tofa albarkacin bakinsu.

A cewar budurwar, kungiyar malaman jami'o'i ta ASUU ba za ta hana kaninta kammala karatu ba duk da cewa ba za su janye yajin aiki ba.

Ta ce ita da kaninta nata sun hau babur ne daga Legas ta hanyar Idi-Iroko, suka hau mota har dai suka shiga kasar ta Benin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel