Jerin Jami'o'in Najeriya 22 Da Suka Zabi A Dakatar Da Yajin Aikin ASUU

Jerin Jami'o'in Najeriya 22 Da Suka Zabi A Dakatar Da Yajin Aikin ASUU

Biyo bayan umurnin da shugabannin kungiyar malaman jami'o'i na kasa, ASUU, sassa da dama na malaman jami'an yanzu sun zabi a dakatar da yajin aikin da suka shafe watanni ana yi.

Deborah Tolu-Kolawale, yar jarida mai aiki da The Punch, ce ta bayyana hakan a rubutun da ta yi a Twitter.

Jami'ar BUK Da Ibadan
Jerin Jami'o'in Najeriya 22 Da Suka Zabi A Dakatar Da Yajin Aikin ASUU. Hoto: PIUS UTOMI EKPEI/, AMINU ABUBAKAR/AFP.
Asali: UGC

A cewar yar jaridar na makarantun gaba da sakandare, ga jerin jami'o'in da suka zabi a janye yajin aikin bisa sharadi ko umurnin kotu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yajin aikin ASUU: Jami'an da suka zabi a dakatar da yajin aikin

  1. Ladoke Akintola University of Technology (LAUTECH)
  2. The Federal University of Technology Akure (FUTA)
  3. University of Benin (UNIBEN)
  4. University Of Nigeria Nsukka (UNN)
  5. Tai Solarin University of Education (TASUED)
  6. Nnamdi Azikiwe University (UNIZIK)
  7. University of Lagos (UNILAG)
  8. Ekiti State University (EKSU)
  9. University Of Calabar (UNICAL)
  10. University of Port Harcourt (UNIPORT)
  11. Federal University of Technology, Owerri (FUTO)
  12. Adekunle Ajasin University
  13. Olabisi Onabanjo University (OOU)
  14. Kano University of Science & Technology
  15. University of Maiduguri (UNIMAID)
  16. University Of Jos (UNIJOS)
  17. Federal University of Agriculture, Abeokuta (FUNAAB)
  18. Alex Ekwueme Federal University
  19. Federal University of Technology Minna
  20. Kebbi State University of Science and Technology Aliero
  21. Usmanu Dan Fodio University Sokoto (UDUS)
  22. Bayero University Kano (BUK)

Kara karanta wannan

Dalla-Dalla: Jerin mutanen da Buhari ya ba lambobin yabo, da abin da hakan ke nufi

OAU ta gaza cimma matsaya

A bangare guda, an gano cewa ASUU na reshen Jami'ar Obafemi Awolowo, Ile-Ife ta gaza cimma matsaya kuma yanzu tana jiran mataki da majalisar zartawa, NEC.

NEC din za ta gana a yau ranar Alhamis, 13 ga watan Oktoba, don yanke shawara kan kuri'un da sassanta suka yanke.

An tattaro cewa Jami'ar Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kebbi, Aliero da Jami'ar Usman Dan Fodio ta Sokoto ta yarda a janye yajin aikin saboda umurnin kotu.

BUK ta zabi a dakatar da yajin aikin bisa sharadi.

Tolu-Kolawole ta ce dukkan sassan ASUU, illa na jami'ar OAU, sun zabi a dakatar da yajin aikin kan sharadi ko kuma umurnin kotu.

Gwamnati Za Ta Baiwa Malaman ASUU N50bn Kudin Alawus, N170bn Kudin Karin Albashi

Punch ta ruwaito cewa za'a mayar da ragamar biyan kudin alawus na ma'aikatan jami'o'in Najeriya hannun majalisar jagorancin jami'o'in gwamnatin tarayya daga 2024.

Kara karanta wannan

2023: Jam'iyya Ta Kori Tsohuwar Shugabar Majalisa, Kwamishina da Wasu Jiga-Jigai Kan Wani Dalili

Hakazalika gwamnati za ta saki kudi naira bilyan hamsin (N50bn) don biyan kudin bashi na alawus da Malaman ke bi kafin lokacin.

Wata majiya cikin majalisar zartaswar ASUU ta bayyana hakan ranar Laraba a birnin tarayya Abuja, rahoton Punch.

Asali: Legit.ng

Online view pixel