Cikakken Jerin 'Yan Najeriya da Suka Karbi Lambar Yabo ta Kasa a 2022 da Abin da Hakan Ke Nufi

Cikakken Jerin 'Yan Najeriya da Suka Karbi Lambar Yabo ta Kasa a 2022 da Abin da Hakan Ke Nufi

A ranar Talata, 11 ga watan Oktoba ne shugaba Buhari na Najeriya ya ba da lambobin yabo na kasa ga wasu fitattu kuma amintattun 'yan Najeriya, wasu 'yan kasar waje ne.

Fitattun da suka yi suna daga cikin wadannan mutanen akwai marigayi shugaban ma'aikatan Buhari, Abba Kyari, gwamna Rotimi Akeredolu na Ondo da darakta janar na kungiyar kasuwanci ta duniya (WTO) Ngozi Okonjo-Iweala.

Jerin wadanda Buhari ya ba lambar yabo
Cikakken jerin 'yan Najeriya da suka karbi lambar yabo ta kasa a 2022 da abin da hakan ke nufi | Hoto: Femi Gbajabiamila
Asali: Facebook

Hakazalika, akwai irinsu shugaban hukumar JAMB, Ishaq Oloyede, ministan ayyuka da gidaje Babatunde Raji Fashola, Sheikh Sani Umar Rijiyar Lemo dai sauransu.

Kalli cikakken jerin anan:

Lambobin yabon da Buhari ya bayar
Cikakken Jerin 'Yan Najeriya da Suka Karbi Lambar Yabo ta Kasa a 2022 da Abin da Kakan Ke Nufi | @gimbakakanda
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Lambobin yabon da Buhari ya bayar
Cikakken Jerin 'Yan Najeriya da Suka Karbi Lambar Yabo ta Kasa a 2022 da Abin da Kakan Ke Nufi | Hoto: @gimbakakanda
Asali: Twitter

Lambobin yabon da Buhari ya bayar
Cikakken Jerin 'Yan Najeriya da Suka Karbi Lambar Yabo ta Kasa a 2022 da Abin da Kakan Ke Nufi | Hoto: @gimbakakanda
Asali: Twitter

Me ake nufi da lambar yabo ta kasa a Najeriya?

An fara wannan al'ada ta ba fitattun 'yan kasa lambobin yabo ne a shekarar 1964 a lokacin mulkin Alhaji Abubakar Tafawa Balewa, inda aka samar da dokar ba da lambar yabo ta kasa.

Kara karanta wannan

Mutane 4 da Aka Taba Ba Su Lambar Yabo, Amma Suka Ki Karba a Tsawon Shekaru 58

Dokar, wacce ta fara aiki a ranar 1 ga watan Oktoban 1963, kafin ma kafa ta a 1964, ta ba da kofar gano wadanda suka yiwa kasa hidima tare da karbar lambar yabo kai tsaye daga hannun shugaban kasa bisa jajircewarsu.

Wadanne lambobin yabo ake bayarwa?

  1. Grand Commander of the Order of the Federal Republic (GCFR)
  2. Grand Commander of the Order of the Niger (GCON)
  3. Commander of the Order of the Federal Republic (CFR)
  4. Commander of the Order of the Niger (CON)
  5. Officer of the Order of the Federal Republic (OFR)
  6. Officer of the Order of the Niger (OON)
  7. Member of the Order of the Federal Republic (MFR)
  8. Member of the Order of the Niger (MON)

Lambar yabo mafi girma

GCFR ce lambar yabo mafi girma da dan Najeriya zai iya samu, kuma kamar an tanadi wannan lambar yabo ce ga shugabannin kasa da wadanda suka taba mulkar kasa, duk da cewa dokar bata bayyana hakan ba.

Kara karanta wannan

Mamaki Yayin Da Gwamnatin Buhari Ta Amince EFCC Ta Gurfanar Ta Shahararriyar Sanatan APC A Kotu

Duk da haka, an samu lokutan da hakan saba a kan Cif Obafemi Awolowo da Moshood Kashimawo Abiola.

Awolowo ya samu lambar yabon GCFR ba tare da zama shugaban kasa a Najeriya ba.

Tsohon shugaban kasa Shehu Shagari ya ba shi wannan lambar yabo ne saboda aikinsa tukuru kafin da kuma bayan samun 'yancin kai a Najeriya.

Hakazalika, a 2018, shugaba Buhari ya ayyana ba marigayi Moshood Abiola lambar yabon GCFR. Abiola ne ya lashe zaben 12 ga watan Yunin 1993 na shugaban kasa.

Kamar Zomo Ne Ke Bin Zaki, Al-Mustapha Ya Ce EFCC, ICPC Ba Za Su Iya Yaki da Cin Hanci da Rashawa Ba

A wani labarin, dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar AA, Hamza Al-Mustapha ya ce hukumomin da aka kirkira a Najeriya domin yakar rashawa ba za su iya yakar rashawan ba.

Da take zantawa da gidan talabijin na Channels a ranar Talata, tsohon hadimin na marigayi Abacha ya ce idan aka zabe a 2023 shi zai inganta hukumomin dake yaki da rashawa a Najeriya.

Kara karanta wannan

Hotuna da Bidiyon Sojan Dake Satar Makamai Yana Kaiwa ‘Yan Bindiga Yayin da Dubunsa ta Cika

A cewarsa:

"A Najeriya, na yi imanin cewa, hukumomin da aikinsu na farko shine kula da tsaro, cin hanci da rashawa a Najeriya ba su wadata ba. Suna da kaskanci sosai; basu da tsari mai kyau."

Asali: Legit.ng

Online view pixel