Bayan Shekaru 21 da Aure, Matar Manomi ta Haifa ‘Yan 5 Bayan Yara 13 da Take dasu

Bayan Shekaru 21 da Aure, Matar Manomi ta Haifa ‘Yan 5 Bayan Yara 13 da Take dasu

  • Hajara Shuaibu, matar manomi mai karamin karfi a jihar Katsina ta zama abun mamaki sakamakon yadda ta haifa yara biyar a lokaci daya kuma a gida
  • Mahaifiyar yara 18 din tun farko ta haifa yara 13 da suka hada da tagwaye biyu kafin ta haifa yara biyar a ranar Laraba, 5 ga watan Oktoba
  • Hajara tace bata taba shan magani ko wani abinci da zai sa ta dinga haihuwa ba kuma bata taba zuwa awo ba don duk yaranta a gida ta haifesu

Katsina- A jihar Katsina, wasu mutane sun fara kwatanta Hajara Shuaibu matsayin matar da tafi kowa haihuwa a Najeriya bayan ta haifa yara 5 a ranar Laraba, 5 ga watan Oktoban 2022.

Hajara Shuaibu
Bayan Shekaru 21 da Aure, Matar Manomi ta Haifa ‘Yan 5 Bayan Yara 13 da Take dasu. Hoto daga BBC Pidgin
Asali: UGC

Yadda matar aure ta haifa yara 18

Kara karanta wannan

Budurwa ta Bude Guruf a WhatsApp, Ta Tara Duk Samarinta Tare da Sanar Musu Zata yi Aure, Ta Fice ta Basu Wuri

Tun farko dai Hajara ta haifa tagwaye har sau biyu,tazo ta haifa yara 9 daban-daban kafin ta haifa yara 5 a lokaci daya a makon da ya gabata.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Bata taba tsammanin zata haifa fiye da jinjiri daya ba don haka rayuwarta yadda ta saba take yi

Hajara bata taba zuwa awo ba kuma ta haifa dukkan yaranta a gida. Wata unguwan zoma ce ta taimaka mata ta haihu.

Ta bayyana cewa an kai ta babban asibitin Funtua domin duba lafiyarta bayan ta haihu a gida.

A bayaninta:

“A gida na haihu amma bayan nan an kai ni asibiti inda aka saka min jini kuma aka ce in huta. Duk sauran haihuwan da nayi a gida nayi. Dukkan yarana a gida na haifesu ba tare da an yi min aiki ba.”

Waye mahaifin yaranta 18?

Kara karanta wannan

Budurwa Ta Yi Murabus Daga Wajen Aikinta A Amurka, Ta Siyar Da Kayayyakinta, Ta Koma Ghana Saboda Namiji

Mijin Hajara manomi ne mai suna Shuaibu Umar kuma ya bayyana cewa biyu daga cikin jariran sun rasu a ranar Alhamis amma sauran ukun da mahaifiyarsu an kai su babbar cibiyar lafiya ta tarayya dak Katsina don samun kula.

Shuaibu manomi ne daga kauyen Doman kuma yace haihuwan nan albarka ce garesa da matarsa. Bata taba shan komai ba don samu haihuwa ba.

Ya bayyana cewa shugaban karamar hukumar Faskari na jihar Katsina ya bashi tallafin N100,000 amma yace zai kara aiko masa da wani tallafin.

Yaushe Hajara tayi aure?

Mahaifin Hajara, Umar Hussaini yace ya aurar da diyarsa ga manomin shekaru 21 da suka gabata.

“Shekarun Hajara 35 kuma na aurar da ita shekaru 21 da suka gabata. A kan haihuwar da take yi, zan iya cewa kyauta ce daga Allah.”

- Yace.

Mata da ‘Yan Yara 30 Sun Yi Shahada, Sun Nutse a Ruwa Za Su Tserewa ‘Yan Bindiga

Kara karanta wannan

Dalilin Da Yasa Na Saci Sabon Jariri A Asibitin ATBUTH Dake Bauchi

A wani labari na daban, Fiye da mutane 30 suka hallaka kwanakin baya a lokacin da suke neman kubuta daga wasu miyagun ‘yan bindiga a kauyen Zamfara.

Jaridar nan ta Vanguard ta rahoto cewa kananan yara da mata da neman tsira da rayuwarsu sun gamu da ajalinsu a tsakiyar makon da ya gabata.

Abin ya faru ne yayin da kwale-kwalen da ya dauko wadannan mutane ya nutse a cikin ruwa. Ana zargin mutane kusan 30 ne suka yi shahada.

Asali: Legit.ng

Online view pixel