Tallafi Na Jiransa: Dan Najeriya Ya Sa A Nemo Masa Mubarak Yusuf, Yaro Makanike Da Ke Zuba Turanci A Bidiyo

Tallafi Na Jiransa: Dan Najeriya Ya Sa A Nemo Masa Mubarak Yusuf, Yaro Makanike Da Ke Zuba Turanci A Bidiyo

  • Wani dan Najeriya na shirin tallafawa Mubarak Yusuf, makaniki mai kwazo da ya nuna hazikancinsa a wani bidiyo da ya yadu
  • Mutumin mai suna Cyprian Kendo ya wallafa bidiyon yaron da ya yadu a Twitter inda ya nemi a nemo masa shi don bashi tallafin karatu kyauta
  • Mubarak ya shahara bayan yaduwar bidiyonsa yana zabga muhawara game da karatun dare da na rana a wani shagon kanikanci

Mubarak Yusuf, hazikin dan Najeriya wanda ke koyon aikin kanikanci na gab da samun taimako.

Mubarak ya dauki hankalin mutane ne bayan wani bidiyonsa yana zuba turanci cike da hikima yayin wata muhawara ya yadu a soshiyal midiya.

Kendo da Mubarak
Tallafi Na Jiransa: Dan Najeriya Ya Sa A Nemo Masa Mubarak Yusuf, Yaro Makanike Da Ke Zuba Turanci A Bidiyo Hoto: Twitter/@KendoCyprian and TikTok/@ayofeliberato.
Asali: UGC

A cikin bidiyon, yaron wanda ke koyon aikin kanikanci ya yi muhawara game da karatun dare da na rana inda yake goyon bayan karatun rana. Legit.ng ce ta wallafa labarin.

Kara karanta wannan

Bacin rana: Wasu mutane sun fusata, sun raba dan luwadi da gangan jikinsa

Mubarak ya fito ya bayar da hujja mai ma’ana cewa karatun dare zai sa dalibai su kama bacci a cikin aji.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bidiyon muhawarar ya yadu

Bayan @ayofeliberato ya wallafa bidiyon a TikTok, nan take ya yadu sannan mutane suka fara tambayar me yasa yaron baya zuwa makaranta.

Sun yi kira ga jama’a da su taimakawa yaron tunda yana da kwazo sosai.

Cyprian Kendo, dan Najeriya wanda ya nemi a nemo masa Mubarak ya amsa wannan kira nasu.

A cewar Kendo, idan an gano yaron, tallafin karatu kyauta na nan yana jiransa.

Kalli wallafarsa a kasa:

Jama'a sun yi martani

@KingJeffFX yace:

“Ka bude masa babban shago a maimakon haka. Ya kamata ku yan Afrika ku dawo daga rakiyar cewa makaranta ce hanyar nasara…a zamanin da ne yake haka, ba yanzu ba”

Kara karanta wannan

Bidiyon yaro mai sana'ar kanikanci dake zuba turanci ya bar jama'a a intanet baki bude

@richard09161477 ya yi martani:

“Daga sigar magana bana tunanin yaron nan dan Najeriya ne ina gamin Dan Uganda ko Kenya ne.”

@OneManMopol101 ya ce:

“Ya iya zantuka kuma yana da hazaka, ya kamata ace yana makaranta ba a shagon kanikanci ba. Allah ya kara budi yallabai.”

Bidiyon Yaro Makanike Na Zuba Turanci Ya Ba Jama’a Mamaki

A baya mun ji cewa, dandazon mutane a shafin TikTok sun kamu da kaunar wani yaro mai suna Mubarak saboda irin kwazon da yake dashi.

Hakan ya fara ne daga wani bidiyon da @ayofeliberato ya yada na lokacin da Mubarak ke karanta wata muhawara da ta dauki hankali ya yadu a intanet.

Kwarewarsa a yaren turanci ta ba jama'a mamaki, wannan yasa suka ce ya yi matukar burge su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel