Wasu Mutane Sun Guntule Kan Wani Bafalasdine Dan Luwadi, Sun Shiga Hannu

Wasu Mutane Sun Guntule Kan Wani Bafalasdine Dan Luwadi, Sun Shiga Hannu

  • 'Yan sanda sun kama wasu mutanen da suka hallaka wani mutum mai ra'ayin tarayya da maza a yankin Falasdinawa
  • Rahotanni daga kafafen yada labaran Isra'ila sun bayyana cewa, an jima ana bibiya tare da yiwa mutumin barazana
  • Mutumin mai suna Ahmad Marhia ya shafe shekaru biyu yana neman mafaka a kungiyar masu irin ra'ayinsa

Wani dan luwadi a yankin Falasdinawa ya bakunci kiyama yayin da wasu mutane suka guntule kansa a yammacin kogin Jordan.

Kafar Labarai ta BBC ta ruwaito cewa, mutumin mai suna Ahmad Abu Marhia ya dadi da fara neman mafaka a dandalin kungiyar masu auren jinsi daya ta kasar Isra'ila a lokacin da ya fara samun barazana a garinsu.

An kashe Ahmad Abu Marhia, dan luwadi
Wasu Mutane Sun Guntule Kan Wani Bafalasdine Dan Luwadi, Sun Shiga Hannu | Hoto: bbc.com
Asali: UGC

Rahoton ya kuma bayyana cewa, tuni 'yan sanda suka kama wasua mutanen da ake zargi da kisa.

Kara karanta wannan

Bakano ya girgiza intanet, ya kera keke napep din da ta ba 'yan Najeriya mamaki

Bidiyon lamarin ya yadu a kafafen sada zumunta

A bangare guda, an samu cece-kuce yayin da bidiyon kisan da aka yiwa Ahmad ya karade kafafen sada zumunta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mutane da dama sun yi ta yada ra'ayoyi da kakalen tushe da dalilin kashe Ahmad, duk da dai 'yan sanda basu tabbatar da dalilin kisan da ya faru a Hebron ba.

Har ya zuwa yanzu dai aba a iya gano yadda Ahmad ya shiga garin ba.

Rahotanni daga kafafen yada labaran Isra'ila sun ce, an sace Ahmad ne kana aka kaishi yamma da kogin Jordan domin hallaka shi.

A bangare guda, iyayensa sun ce ya kan kai ziyara yankin Hebron a lokaci zuwa lokaci don ganawa da su, rahoton Daily Mail.

Ahmad dai ya shafe shekaru biyu a kasar Isra'ila yana neman mafaka da takardun samun damar tsallaka kasashen waje tun bayan tumbazatsar barazanar da yake samu, kungiyoyin kare 'yancin 'yan luwadi da madigo.

Kara karanta wannan

Biliyoyin da Shugabanni Suka Wawure Daga Najeriya Suna Dankare a Turai, Buhari

Hotunan Yadda Wani Bakano Ya Kera Keke Napep Tun Daga Tushe

A wani labarin, wasu hotuna da jarida Punch ta yada a kafar Twitter sun nuna wani matashi dan jihar Kano da ya kera keke napep tun daga tushe.

An ga hoton matashin mai suna Faisal a jikin keke napep din aka ce ya kera.

Mutane da dama a kafar sada zumunta sun yi martani bayan ganin hazikin matashin dan Najeriya ya kera daya daga abubuwan sufuri da ake amfani dashi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel