Kano: Yadda Mata Ke Tururuwar Zuwa Siyan Kai, Kafa da Hanjin Kaji, Har da Kusa Ba Hammata Iska

Kano: Yadda Mata Ke Tururuwar Zuwa Siyan Kai, Kafa da Hanjin Kaji, Har da Kusa Ba Hammata Iska

  • Legit.ng Hausa ta kutsa kasuwar Tarauni inda ta ga mata cincirindo suna siyan kai, kafa da hanjin kaji a wurin masu figar kajin
  • Mun zanta da Malam Sabi’u Muhammad wanda fitaccen dillali ne a sana’ar kuma yace mafi yawan kwastomominsa matan Kano ne
  • Ya sanar da cewa shekarun 14 zuwa 15 yana sana’ar inda yake siyar da kowanne N50, N60 har zuwa N100 bisa la’akari da girmansu

Kano- Kamar yadda aka saba ana kiran Kano ta Dabo, cigari kuma tumbin giwa ko da me ka zo an fi ka, hakan take kuwa. Kano gari ne da ya tara manyan ‘yan kasuwa wanda ko tafiya kake a titunansu zaka san ta cancanci zama cibiyar kasuwancin arewacin Najeriya.

Legit.ng Hausa ta kai ziyara kasuwar Tarauni inda ta ga wani nau’in kasuwanci na siyar da kai da kafafun kaji har da kayan cikinsu.

Kara karanta wannan

Isah Barde, Dan Kanon Da Ya Kera Mutum-Mutumi Mai Motsi Da Kwali Ya Samu Tallafin Karatu

Kai da Kafan Kaji
Kano: Yadda Mata Ke Tururuwar Zuwa Siyan Kai, Kafa da Hanjin Kaji, Har da Kusa Ba Hammata Iska
Asali: Original

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Legit.ng Hausa ta zanta da Malam Sabi’u babban ‘dan kasuwa kuma dillalin kai da kafafun kaji har da hanjinsu inda ya warware sirrin dake cikin sana’arsa da wasu ke yi wa kallon uku kwabo.

Malam Sabi’u Muhammad yace ya fara ne da sana’ar figar Kajin a kasuwar Tarauni. Ya dauka shekaru goma sha hudu zuwa sha biyar yana wannan sana’ar.

“Gaskiya wannan sana’ar mu ita muka sa gaba kuma da ita muka dogara. Idan ki ka ga ba mu fito kullum ba, toh halayyar ‘dan Adam ce ta rashin lafiya da wasu ‘yan uzurirrika da ba za a rasa ba. In banda hakan kullum sai mun hallara a kasuwa a cikin tsawon wadannan shekarun.”

- Yace.

Kamar yadda Legit.ng Hausa ta gani da idonta a safiyar Talata wurin karfe 10 na safe, mata ne suka yi cincirindo suna tsaye domin jiran samun kai da kafafun kajin har da hanjin.

Kara karanta wannan

A Shekaru 3 a Ofis, Mun Kammala Ayyuka Fiye da 2000 a Ma’ikatarmu – Isa Pantami

Malam Sabi’u Muhammad yace hakan ce ta saba kasancewa a kowacce rana kuma ana siyar da kai da kafa a kan N50, N60 har zuwa N100 amma duba da irin girmansu ne suke siyarwa.

Suna kuma cire kai da kafan kajin da za a siyar da tsokarsu ne sannan su siyarwa da jama’a.

“Kinsan rayuwar kowa kashi-kashi ce, wani za ki ga arzikinsa ya kai ya siya kaza, wani arzikinsa a iya kai da kafan ya tsaya. Toh mafi akasari an fi siyan kai da kafan fiye da masu siyan tsokar.
“Muna amfani da siyan kazar da ake yi mu siyar da kai da kafan don ba zai yuwu mu yanka kaji mu siyar da kai da kafa a bar mu da gangan jikinsu ba. Siyan kaza muke mu yanka, mu kasa mu siyar da kai da kafan, idan ta kare mu sake yin hakan.”

- Dillali kai da Kafan Kaji ya kara da cewa.

Kara karanta wannan

Yajin-aiki: Kotu Ta Fadawa ASUU da Gwamnati Yadda Za Su Shawo Kan Sabaninsu

Malam Sabi’u yace akwai lokutan da kai da kafan ke wahalar samu, wasu kan zo tun safe har kusan yamma su rasa. Wasu lokutan kuwa kamar bayan sallah ana samun shi har yayi kwantai.

Malam Sabi’u yace mata na yin cincirindo kuma har su nemi bai wa hammata iska idan da zasu samu sarari, sai dai su masu siyarwan suna lura da kwastomomi yadda komai ke tafiya daidai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel