Borno: Mayakan Boko Haram Sun Kai Hari Chibok, Sun Sheke Rai 3

Borno: Mayakan Boko Haram Sun Kai Hari Chibok, Sun Sheke Rai 3

  • Wasu 'yan ta'addan Boko Haram sun kai mummunan farmakin kauyen Njilang dake karamar hukumar Chibok a jihar Borno
  • Kamar yadda Zagazola Makama ya bayyana, sun budewa jama'ar yankin wuta dake gudun ceton rai inda suka halaka rayuka 3
  • Ba su tsaya a nan ba, 'yan ta'addan Boko Haram din sun balle shaguna tare da kwashe kayayyaki kafin sun bankawa gidaje wuta

Chibok, Borno - A kalla mutum uku ne aka tabbatar da mutuwarsu yayin da wasu da ake zargin 'yan Boko Haram ne suka kutsa kauyen Njilang dake gundumar Whuntafu a karamar hukumar Chibok ta jihar Borno.

'Yan ta'addan sun kutsa kauyen Njilang wurin karfe 2:34am na ranar Litinin kuma suka bude wuta kan mazauna yankin dake kokarin tserewa inda suka halaka mutum uku tare da yashe shaguna kafin su bankawa gidaje wuta.

Kara karanta wannan

Ummita: Kotu ta Dage Sauraron Shari'ar 'Dan Chana da Ya Halaka Budurwarsa Saboda Rashin Tafinta

Taswirar Borno
Borno: Mayakan Boko Haram Sun Kai Hari Chibok, Sun Sheke Rai 3. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Kamar yadda Zagazola Makama, kwararren a fannin kiyasin tsaro da kuma yaki da ta'addanci a yankin Chadi ya bayyana a shafinsa na Twitter, lamarin ya faru a ranar Litinin ne a Borno.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan Ta'adda 29 Sun Mutu Yayi Wata Mummunar Arangama Tsakanin Boko Haram da ISWAP

A wani labari na daban, mayakan kungiyar ISWAP a daren Juma'a sun yi arangama da 'yan ta'addan Boko Haram a karamar hukumar Bama ta jihar Borno.

ISWAP wani tsagi na Boko Haram da suka ware tare da kafa kungiyarsu bayan an samu hargitsin shugabanci. Abubakar Shekau, shugaban Boko haram ya sheka lahira bayan arangamarsu da ISWAP a 2021.

Kamar yadda Zagazola Makama, kwararre a yaki da ta'addanci ya bayyana, 'yan ta'adda 29 sun rasa rayukansu sakamakon arangamar a Borno.

Wasu mayakan ISWAP da suka samu shugabancin Ba'ana Chigori sun kai samame maboyar Boko Haram dake Gaizuwa inda aka fi sani da Gabchari, Mantari da Mallum Masari, wanda hakan ya janyo artabun sa'o'i har zuwa safiyar Asabar.

Kara karanta wannan

Mutane 3 Sun Mutu, Wasu Da Dama Sun Jikkata Yayin da Mayakan Boko Haram Suka Farmaki Borno

Wani jami'in sirri ya sanar da Zagazola Makama cewa an yi wa 'yan Boko Haram harin kwantan bauna.

"'Yan ta'addan ISWAP sun fi karfin kungiyoyin hamayyar wadanda suka dira wa ba-zata, kuma an halaka da yawa daga cikinsu yayin da wasu suka race cikin daji don gudun mutuwa."

- Jami'in yace.

Asali: Legit.ng

Online view pixel