Sarkin Bashar, Dan Uwan Mataimakin Shugaban Majalisar Tarayya Ya Rasu
- Yayan mataimakin kakakin majalisar dokokin tarayya, Hon Ahmed Idris, Wase, watau Alhaji Adamu Idris ya rasu
- A wata sanarwa da sakataren watsa labaransa ya fitar, yace marigayin wanda shi ne Sarkin Bashar a Jos, ya rasu ne yana da shekaru 96
- Sanarwan ta ƙara da cewa za'a yi wa mamacin jana'iza kamar yadda Addinin Musulunci yau tanadar yu Lahadi
Jos, Plateau - Mataimakin shugaban majalisar wakilan tarayya, Ahmed Idris Wase, ya yi rashin ɗan uwansa, Alhaji Adamu Idris.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da Sakataren watsa labarai na ɗan majalisar, Umar Muhammad Puma, ya fitar ranar Lahadi.

Asali: Twitter
A cewar Sanarwar, Marigayin ya kwanta dama ne yau Lahadi, 25 ga watan Satumba, 2022 a Jos, babban birnin jihar Filato, yana ɗan shekara 96 a duniya.

Kara karanta wannan
Dailin Da Yasa Na Yi Shiru Game da Rikicin Atiku da Gwamna Wike, Saraki Ya Magantu
Sanarwan ta ce:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
"Cikin yanayin baƙin ciki da takaici muke sanar da rasuwar Sarkin Bashar, Alhaji Adamu Idris; babban yaya ga mataimakin kakakin majalisar wakilai ta ƙasa, Rt. Hon. Ahmed Idris Wase."
"Ya riga mu gidan gaskiya a Jos a awannin farko na yau (Lahadi 25 ga watan Satumba, 2022) yana da shekaru 96 a duniya."
"Ya rasu ya bar mata huɗu da 'ya'ya da jikoki da dama. Za'a masa Jana'iza yau a garin Bashar da ke jihar Filato kamar yadda addinin Musulunci ya tanada."
Wani Matashi ya mutu a wurin bikin karin shekara
A wani labarin kuma Wani Matashi Dan Shekara 21 Ya Mutu a Wurin Shagalin Bikin Karin Shekara a jihar Legas
Wani matashi ɗan shekara 21 a duniya, Micheal Arigbabuwo, ya rasa rayuwarsa a wurin shagalin bikin murnar zagayowar ranar haihuwa bayan haɗa manyan miyagun kwayoyi da suka sha ƙarfinsa.

Kara karanta wannan
Yanzu-Yanzu: Bayan Tona Asirin Wasu Jiga-Jigan PDP, Gwamna Wike Ya Yi Sabuwar Tafiya
Mai magana da yawun rundunar yan sanda reshen jihar Legas, SP Benjamin Hundeyin, shi ne ya tabbatar da haka a shafinsa na Tuwita ranar Lahadi.
Asali: Legit.ng