An Yanke Wa Jarumin Fim Da Ya Bindige Mahaifiyarsa Har Lahira Hukunci A Kotun Koli

An Yanke Wa Jarumin Fim Da Ya Bindige Mahaifiyarsa Har Lahira Hukunci A Kotun Koli

  • Kotun a Canada ta yanke hukuncin daurin rai da rai ga jarumi Ryan Grantham bayan ya amsa laifin halaka mahaifiyarsa
  • Jarumin dan shekara 24 ya bindige mahaifiyarsa Barbara White a shekarar 2020 a gidansu a yayin da ta ke wasa da Piano
  • An kuma gano gawar wani mutum da matarsa a Jihar Anambra da ake zargin dan su ne ya kashe su ya tsere

Canada - An yanke wa jarumin fim na kasar Canada Ryan Grantham hukuncin daurin rai da rai bayan amsa laifinsa na kashe mahaifiyrsa, Barbara White a shekarar 2020, Vanguard ta rahoto.

Mai shari'a Kathleen Ker na Kotun Koli na British Columbia da ke Vancouver a ranar Laraba ta yanke wa jarumin dan shekara 24 hukucin.

Ryan Grantham
An Yanke Wa Jarumin Fim Da Ya Bindige Mahaifiyarsa Har Lahira Hukunci A Kotun Koli. Hoto: @VanguardNGA.
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Rashin Tausayi: Wani Dalibin Najeriya Ya Halaka Mahaifinsa Da Mahaifiyarsa, Ya Rufe Gawarsu A Daki Ya Tsere

Ya amsa laifin da ake tuhumarsa na kasa amma na mataki na biyu bayan da farko an gurfanar da shi kan zargin kisa na mataki na farko.

Shekarun Grantham 21 a lokacin da ya bindige mahaifiyarsa a kai a yayin da ta ke wasa da Piano a gida a ranar 31 ga watan Maris.

Kisan ya faru ne a gidansu da ke Squamish, arewacin Vancouver.

Grantham ya so ya kashe farai ministan Canada, Justin Trudeau

Masu bincike sun kuma ce ya yi niyyar ya kashe Farai Ministan Canada Justin Trudeau amma a maimakon zuwa gidan Trudeau, ya shiga mota ya kai kansa hedkwatar yan sanda ya mika kansa.

Grantham na fama da matsalar kwakwalwa - Mai Shari'a Ker

Ker ta bayyana a kotun cewa Grantham na fama da matsalolin kwakwalwa kuma a lokacin 'yana fama da matsanancin damuwa' har zuwa lokacin da ya aikata laifin.

Wani Dalibin Najeriya Ya Halaka Mahaifinsa Da Mahaifiyarsa, Ya Rufe Gawarsu A Daki Ya Tsere

Kara karanta wannan

Najeriya Ta Shigesu: Farashin Danyen Man Ya Fadi A Kasuwar Duniya

A wani rahoton, wani dalibi a makarantun Jihar Anambra da ba a riga an gano shi ba ya halaka mahaifinsa da mahaifiyarsa ya bar gawarsu a cikin daki.

Lamarin ya faru ne a garin Nnewi na Jihar Anambra kamar yadda The Punch ta rahoto.

An tattaro cewa gawar wadanda suka rasun ya fara rubewa a lokacin da makwabta suka gano su saboda wari da ke fitowa daga dakinsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel