Wani Ginin Bene Ya Ruguje a Jihar Filato, Jama’a Sun Shiga Tashin Hankali

Wani Ginin Bene Ya Ruguje a Jihar Filato, Jama’a Sun Shiga Tashin Hankali

  • An samu rugujewar ginin bene a jihar Filato, alamu na nuna an yi asarar dukiya mai yawa a jiya Lahadi
  • Shaidun gani da ido sun bayyana yadda lamarin ya faru, amma sun ce an yi sa'a ba a samu asarar rai ba
  • Ana yawan samun rushewar gine-gine a Najeriya tun farkon shekarar nan, lamarin dake kara kawo cece-kuce

Bukuru, jihar Filato - A daren jiya Lahadi 18 ga watan Satumba ne labari ya shigo na rugujewar wani bene a Bukuru, kusa da Jos a jihar Filato a Arewa masu tsakiya a Najeriya.

Sai dai, an yi sa;a, wani shaidan gani da ido ya ce ba a samu asarar rai ba, inji jaridar Daily Trust.

Ginin dake kusa da Bukuru Mini Stadium yana da shagon siyayya na zamani da kuma ofisoshi a hawan sama.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Wani Bam Ya Fashe a Babban Birnin Jihar Arewacin Najeriya

Yadda bene ya ruguje a jihar Filato
Wani Ginin Bene Ya Ruguje a Jihar Filato, Jama’a Sun Shiga Tashin Hankali | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Mai ginin, wani Mr Moses Pam da ya zanta da manema labarai ya godewa ubangiji bisa sa'ar da ya yi ba ya cikin ginin, kuma ya tsira.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa:

"Da misalin karde 6:30 na yamma a ranar Lahadi, na shiga domin kirga kayan dake cikin shagon.
"Yayin da nake cikin shagon, na ji wani irin kara sai na fita da gudu na rufe shagon.
"Na fara tafiya sai kuma na ji wani ihu, da na juya sai naga kura ta ko'ina. Wannan kenan abin da nake iya tunawa."

Dalilin faduwar ginin

Wani ganau ya shaidawa kamfanin dillacin labaran Najeriya ya ce akwai yiwuwar ruwan sama ne musabbin rugujewar ginin, rahoton Vanguard.

Tawagar hukumar ba da agajin gaggawa (NEMA) da take wurin da lamarin a faru ta godewa Allah danin ba a rasa rai ba.

Kara karanta wannan

Al-Mustapha Ya Fashe Da Kuka Ya Zubar Da Hawaye Kan Rashin Tsaro A Najeriya

Hakazalika, hukumar ta kuma shawarci masu gine-gine da suke yin masu inganci.

Wasu Sun Farmaki Coci, Sun Lakadawa Fasto Duka Yayin da Yake Wa’azin Ranar Lahadi

A wani labarin, wani coci a kauyen Shikal na karamar hukumar Lantang ta Kudu ya fuskanci farmakin wasu mutanen da suka badda kamanni da shigar dodanni a ranar Asabar 17 ga watan Satumba.

Rahoton da muke samu daga jaridar Daily Trust ya bayyana cewa, wadanda suka farmaki cocin sun yiwa masu bauta da fastonsu bulala tilis.

Baya ga cin zarafin fasto da mabiyansa tare da watsa kowa dake cikin cocin, an ce sun kuma yi kaca-kaca da kayan kidan cocin da sauran abubuwa masu amfani.

Asali: Legit.ng

Online view pixel