Wani Dan Najeriya Ya Je Siyayya Da Kudi Yar N10 Cike Da Jaka, Bidiyon Ya Haddasa Cece-kuce

Wani Dan Najeriya Ya Je Siyayya Da Kudi Yar N10 Cike Da Jaka, Bidiyon Ya Haddasa Cece-kuce

  • Wani bidiyo da ke yawo a shafukan soshiyal midiya ya nuno wani dan Najeriya da yaje siyayya da kudi yar naira 10 cike da jaka
  • Mai karban kudin da ya tarbe shi ya kadu lokacin da matashin ya mika masa damin kudin
  • Masu amfani da soshiyal midiya da dama da suka yi martani sun yarda cewa kirga irin wannan kudi ba abu bane mai sauki

Wani bidiyo na wani mutum da yaje siyayya da damin kudi yar naira 10-10 ya baiwa masu amfani da TikTok mamaki.

Dan gajeren bidiyon da aka gani a TikTok din ya sa mutane tambayar dalilinsa na zuwa siyayya da naira mafi kankanta cikin kudi.

Matashi da jakar kudi
Wani Dan Najeriya Ya Je Siyayya Da Kudi Yar N10 Cike Da Jaka, Bidiyon Ya Haddasa Cece-kuce Hoto: TikTok/@ochulo_ways.
Asali: UGC

Abun mamaki, mutumin ya zubo bandir-bandir din naira 10-10 a cikin jakar Louis Vuitton sannan ya bude shi a hankali cikin mutumci a gaban mai karbar kudin.

Kara karanta wannan

Bayan Kisan Ummita, Budurwa ta Fallasa Yadda Take Warwarar Kudin Saurayinta Dan Kasar Waje, Tana Neman Shawara

Masu amfani da TikTok sun tausayawa mai karban kudin wanda zai shafe tsawon lokaci wajen kirga kudin masu yawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kalli bidiyon a kasa:

Masu amfani da TikTok sun yi martani

A halin da ake ciki, bidiyon ya ja hankalin mutane inda suka je sashin sharhi domin bayyana ra’ayoyinsu. Kalli wasu daga cikin martanin a kasa:

@bimbolawa ta ce:

“Idan da nice mai karbar kudin kawai kuka zan fashe da shi.”

Xpensive_Pablo ya yi martani:

“Wannan nine idan zani kauyena a wannan Kirsimetin.”

@bummsyofficial ta tambaya:

“Wani irin wawan kudi kake zuwa siyayya da shi.”

@Din ya ce:

“Wannan gayen! Ni fushi zan yi maka fa.”

@Sting Carter ya ce:

"A in aka samo kudin?"

Ki Sallame Ta: Wata ‘Yar Aiki Ta Gabatarwa Uwar Dakinta Tsabar Kudi N100k, Bidiyon Ya Ja Hankalin Mutane

A wani labarin, Afolashade Shakirat, wata yar Najeriya ta ba mutane mamaki bayan tace yar aikinta ta bata tsabar kudi har N100k.

Kara karanta wannan

Yajin ASUU: An kai makura, dalibai sun toshe hanyar filin jirgin sama suna zanga-zanga

Afolashade ta bayyana cewa yar aikin tace tana ta daukar kudinta ne sannan ta taimaka mata wajen tara su.

Mutane da dama sun sha mamaki amma bata sauke bidiyon ba wanda ta wallafa a kan TikTok.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng