Ki Sallame Ta: Wata ‘Yar Aiki Ta Gabatarwa Uwar Dakinta Tsabar Kudi N100k, Bidiyon Ya Ja Hankalin Mutane

Ki Sallame Ta: Wata ‘Yar Aiki Ta Gabatarwa Uwar Dakinta Tsabar Kudi N100k, Bidiyon Ya Ja Hankalin Mutane

  • Afolashade Shakirat, wata matashiya yar Najeriya ta ba da labarin yadda yar aikinta ta bata tsabar kudi har N100,000
  • A cewarta, yar aikin tace tana ta daukar kudin ne daga wajenta don ta tayata tarawa sannan yanzu ta yanke shawarar dawo mata da shi
  • Mutane na ta bata shawarwari game da abun da yakamata ta yiwa yar aikin saboda bata yi tsammanin kudin ba kwata-kwata

Afolashade Shakirat, wata yar Najeriya ta ba mutane mamaki bayan tace yar aikinta ta bata tsabar kudi har N100k.

Afolashade ta bayyana cewa yar aikin tace tana ta daukar kudinta ne sannan ta taimaka mata wajen tara su.

Budurwa da kudi
Ki Sallame Ta: Wata ‘Yar Aiki Ta Gabatarwa Uwar Dakinta Da Tsabar Kudi N100k, Bidiyon Ya Ja Hankalin Mutane Hoto: TikTok/@slimheadies01 and Bloomberg/Getty
Asali: UGC

Mutane da dama sun sha mamaki amma bata sauke bidiyon ba wanda ta wallafa a kan TikTok.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Yadda Yar Najeriya Mazauniyar UK Ta Fatattaki Mijinta Daga Gida Saboda Ya Kira Mata Yan Sanda

Ta tambayi mabiyanta game da abun da yakamata ta yiwa yar aikin. Ra’ayi sun rabu biyu a yanzu yayin da wasu mutane ke cewa kawai ta barwa yar aikin kudin tunda ta nuna gaskiya sosai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu sun shawarceta da ta bukaci yar aikin ta kawo sauran kudin tunda watakila ta dauka fiye da haka. Wata ta shawarceta da ta sallami yar aikin.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

@——Debby ta ce:

“Tambayeta ina sauran yake.”

@chinonyesophy ta yi martani:

“Ki yi tunani da ace kin ga N100k a jakarta, tun ma kafin ki gano cewa tana tayaki tarawa ne. za ki zargeta da sata.”

@Faithful720 tace:

“Hakan na nufin kina kula da ita da so da kauna. Kawai ki bata wani abu.”

@sophisti1 ta ce:

“Ki bata toshiyar baki kan fadar gaskiya.”

Kara karanta wannan

Budurwa Tayi wa Banki Fashi Don ta Samu Kudin Maganin Kansar 'Yar Uwarta

@wealthyuyi288 ta ce:

“Haka diyata ke yi kodayaushe idan nayi korafin bani da kudi sai ta shiga ciki sannan tace momi kina da kudi karba.”

Bidiyon Yadda Aka Fallasa Wata Budurwa Da Ke Bara Da Jinjirin Karya A Lagas

A wani labari na daban, yan Najeriya sun kadu bayan ganin wani bidiyo na wata matashiyar budurwa da ke amfani da jaririn bogi tana bara da rokon kudi a jihar Lagas.

A cikin bidiyon, matashiyar budurwar ta nannade wani abu a tsumman jego sannan tana lallashinsa kamar yaro.

Amma mutumin da take rokon kudin a wajensa shima dan Lagas ne wanda ya san kan abun da suke yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel