Kurma Ya ba Jama'a Mamakin Yadda Ya Tashi Mata 2 'Yan Gida Daya Kuma Yayi Wuff Da Su

Kurma Ya ba Jama'a Mamakin Yadda Ya Tashi Mata 2 'Yan Gida Daya Kuma Yayi Wuff Da Su

  • Wani mutumin kasar Rwanda ya baiwa makwabtansa da yan uwa mamaki ta kan yadda ya shawo kan yan mata biyu yan gida daya kuma yayi wuff da su
  • Essien na zaune lafiya da matarsa Nabanti sai daga bisani kanwarta Petronilla ta dawo cikinsu bayan aurenta ya mutu
  • Su dukka ukun suna zaune a gida daya, suna kwanciya a gado daya, su ci abinci tare sannan suna raba ayyukan gida a tsakaninsu

Rwanda - Masu iya magana sun ce da dadin baki ake siye zukatan mata, amma wani mutumin kasar Rwanda wanda ya kasance kurma ya baiwa mutane da dama mamaki kan yadda ya shawo kan wasu mata biyu cikin sauki don su aure shi.

Miji da matansa
Kurma Ya ba Jama'a Mamakin Yadda Ya Tashi Mata 2 'Yan Gida Daya Kuma Yayi Wuff Da Su Hoto: Afrimax English.
Asali: UGC

Auren Petronilla ya mutu

Mutumin wanda bai tara dukiyar azo a gani ba ya fara auren Mabanti Maliya kuma Allah ya albarkacesu da yara uku.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Wata cuta ta kama kama Nnamdi Kanu a hannun DSS, inji lauyansa

Wata hira da Afrimax English ya bayyana cewa daya daga cikin yaran yayi mutuwar ban mamaki, amma sauran suna nan kuma babban cikinsu mai shekarunsa 20 yana rayuwa a wata uwa duniya. Dayan mai shekaru 19 yana nan a gaban iyayensu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wata rana sai kanwar Habinra Petronilla ta zo gidansu tana mai sanar dasu cewa aurenta ya mutu sai kuma dukkansu suka yanke shawarar zama tare.

Mijina yayi mata ciki

“Maimakon ta koma gida, zai ta zo nan. Mijina ya fada tarkon sonta sannan yayi mata ciki, sun fada mun sai kuma muka yanke shawarar zama tare,” in ji Nabanti.

Ta kara da cewa:

“Muna raba komai tare, mutumin, gado, da abinci. Muna matukar son junanmu.”

Mutumin mai shekaru 52 da iyalinsa na farko suna rayuwa ne a wani gida dan karami amma daga bisani ya nemi wasu kudade sannan ya gina katon gidan laka a gabar tafkin Kivu inda dukkansu suke zaune tare.

Kara karanta wannan

Yadda saurayin diyata dan China ya shiga har gida ya caccaka mata wuka, inji mahaifiyar Ummita

“Wasu abubuwa kawai haka Allah ya kaddara su,” in ji Petronilla Maliya.

Dan uwan Essien bai goyi bayan sabon auren ba

Dan uwan Essien Sakabe Calvin bait aba tsammanin dan uwansa zai kara aure ba kuma ya yi adawa da tsarin. Abokai da makwabtansu sun kadu da lamarin.

“Koda dai na yi adawa da tsarin ina ganin ban yi daidai ba saboda dan uwana yana adalci a tsakanin matansa. Baya ga talauci, babu wani matsala ko rashin jituwa,” cewar Calvin.
“Babu matsala su wanene mu da za mu raba mutanen da ke son junansu?” ya kara da cewa.

Mutumin da matansa manoma ne wadanda ke noma a kullun kuma suna kiwon dabbobi irinsu akuyoyi.

Ina danasani: Budurwa Mai Da Al’aurar Namiji Da Mace Ta Koka Bayan Ta Cire Daya A Bidiyo

A wani labari, wata matashiya yar Najeriya ta tuna halin da ta shiga bayan ta cire daya daga cikin al’urarta guda biyu.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Hirar Karshe Da Budurwar Da Dan China Ya Kashe Tayi Da Kawarta, Ya Kasance Akan Mutuwa

Budurwar mai suna @ifyberry1 a TikTok ta ce an haifeta a matsayin mata-maza wato tana dauke da al’aurar namiji da mace.

A kwanaki, sai ta yanke shawarar cire daya daga cikin al’aurar amma nan take ta fara danasanin matakin da ta dauka bayan aikin gama ya gama.

Asali: Legit.ng

Online view pixel