Ana Harin Fetur Ya Koma N500, ‘Yan Kasuwa Sun Ci Buri da Matatun Fatakwal da Dangote

Ana Harin Fetur Ya Koma N500, ‘Yan Kasuwa Sun Ci Buri da Matatun Fatakwal da Dangote

  • ‘Yan kasuwa sun fara hango sauki yayin da ake shirin kammala gyara-gyaren matatar man gwamnati da ke Fatakwal
  • Idan abubuwa sun zo yadda ake so, ana tunanin litar man fetur zai iya saukowa zuwa N500 daga sama da N600 a yau
  • Ana ganin tasirin saukar Dala da tace danyen mai a matatun gida zai jawo fetur da aka dogara da shi ya rage tsada sosai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Rivers - ‘Yan kasuwa sun fara shirin daukar tacaccen mai daga matatar kamfanin NNPCL da ake daf da kammala gyarawa a Fatakwal.

Ana tunani ba da dadewa ba kamfanin mai na kasa watau NNPCL zai umarci matatar ta fara tace danyen mai, a cigaba da yin aiki.

Kara karanta wannan

Matatar Dangote ta rage farashin mai ne saboda rashin inganci? Gaskiya ta fito

Gidan mai
Fetur zai iya dawowa N500 a gidan mai a Najeriya Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Matatar Fatakwal za ta karya farashin fetur?

Punch ta ce wannan zai jawo farashin man fetur ya sauko sosai a kasuwa bayan tashin da ya yi a sakamakon janye tallafi a 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hasashen ‘yan kasuwan ya nuna idan matatar ta Fatakwal ta fara aiki da kyau ana tace danyen mai, litar man fetur za ta koma N500.

Matatar gwamnatin za ta iya yin sanadiyyar karya kudin man fetur wanda Legit ta fahimci ana saye tsakanin N620 zuwa N770 a yau.

Za a samu fetur a matatar Fatakwal

Rahoton ya ce kungiyar IPMAN ta reshen jihar Ribas ta ziyarci matatar gwamnatin domin ganin inda aka kwana wajen aikin gyaran.

Jami’in hulda da jama’a na kungiyar IPMAN ta ‘yan kasuwan, Ukadike Chinedu, ya shaidawa duniya cewa aikin ya yi nisa sosai.

Saboda haka ne ‘yan kasuwan suka fara shirin yadda za a su rika sayen fetur suna saukewa a matatar a farashi mai rangwame.

Kara karanta wannan

"Allah kaɗai ke ba da mulki," Atiku ya mayar da martani kan zargin cin amana a taron NEC

Daily Trust ta rahoto cewa gyaran da ake yi ya kusa zuwa karshe, matatar za ta fara tace fetur, dizil da sauran sinadarai daga mai.

Man fetur a matatar kamfanin Dangote

Bayan haka, ‘yan kasuwan suna ganin zuwa lokacin da matatar Dangote za ta fara fito da fetur a watan Mayu, kudin lita zai sauka.

Shugaban IPMAN na kasa, Abubakar Maigandi yana ganin Dangote zai iya saida litar fetur a kan N500 idan kayan shi suka fara fitowa.

Dizil ya sauko, fetur zai bi sahu?

Ana da labari zuwa yanzu matatar Dangote ta jawo litar dizil ta sauka zuwa N1200 a kasuwa daidai lokacin da Naira ta tashi kan Dala.

A dalilin haka aka ji Mai girma Bola Tinubu ya yabawa attajirin Afrikan. Shugaban kasar ya ce wannan zai kawo saukin farashin kaya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel