Dan Takarar Shugaban Kasa Ya Bayyana Lokacin Da Yajin Aikin ASUU Zai Zo Karshe

Dan Takarar Shugaban Kasa Ya Bayyana Lokacin Da Yajin Aikin ASUU Zai Zo Karshe

  • Kola Abiola ya bayyana cewa gwamnatin tarayya za ta magance rikicinta da malaman ASUU watanni biyu kafin zabe
  • Abiola ya ce za a kawo karshen yajin aikin ne don dalibai da dama su samu damar yin zabe saboda zai zamana sun yi rijista ne a gida
  • Dan takarar wanda ke rike da tutar Peoples Redemption Party ya kuma bayyana cewa yana nan a cikin tsaren shugaban kasa na 2023 don lashe zabe

Ogun - Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Redemption Party (PRP), Kola Abiola, ya bayyana cewa za a kawo karshen yajin aikin da ke gudana na malaman ASUU watanni biyu kafin babban zaben 2023.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Kola wanda ya magantu a wajen binne marigayi dan takarar gwamna na jam’iyyar PRP a jihar Ogun, David Bamgbos, ya ce yana takarar shugaban kasa ne don dakile tsarin.

Kara karanta wannan

Tun Yanzu, Atiku Abubakar Ya Fara Tattara Sunayen Wadanda Zai Ba Mukamai

Kola Abiola
Dan Takarar Shugaban Kasa Ya Bayyana Lokacin Da Yajin Aikin ASUU Zai Zo Karshe Hoto: Kola Abiola
Asali: UGC

Ya kuma jadadda cewa ya fito takara ne don lashe babban zaben shugaban kasa na 2023 karkashin jam’iyyarsa ta PRP.

Ya ce ta hanyar lashe zaben shekara mai zuwa, zai maimaita nasarar mahaifinsa, marigayi MKO Abiola, a lokacin zaben 12 ga watan Yunin 1993.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Ban damu ba. Idan suka shirya magance yajin aikin, za su aikata haka. Kada ku yi mamaki cewa watanni biyu kafin zaben, za su magance shi don yawancinku su samu damar yin zabe saboda zai zamana kunyi rijista a gida. Kada ku damu a kan haka.”

Tinubu Ya Samu Gagarumin Goyon Baya Daga Wani Shahararren Malamin Addini, Ya Ce Shine Zai Gyara Najeriya

A wani labarin kuma, shugaban kungiyar Young Professionals of Nigeria (YPN), Fasto John Desmond, ya nuna goyon bayansa ga dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

Kara karanta wannan

Duk Karya Ce, APC Tayi Watsi Da Zaben Yanar Gizo Na Cewa Peter Obi Yafi Samun Karbuwa

Desmond ya yi kira ga yan Najeriya da su zabi Tinubu a matsayin shugaban kasa a babban zaben 2023 mai zuwa.

Ya yi kiran ne Umuahia, jihar Abia, yayin wani rangadi na wayar da kan matasan kungiyar YPN wadanda suke mambobin APC a fadin kudu maso gabas, jaridar The Nation ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng