Duk Karya Ce, APC Tayi Watsi Da Zaben Yanar Gizo Na Cewa Peter Obi Yafi Samun Karbuwa

Duk Karya Ce, APC Tayi Watsi Da Zaben Yanar Gizo Na Cewa Peter Obi Yafi Samun Karbuwa

  • Jam'iyyar APC ta yi martani kan zaben yanar gizo dake nuna cewa Peter Obi ya fi samun karbuwa wajen jama'a
  • APC tace ko a shekarar 2015 da 2019 kungiyar ta ce Buhari bai zai ci zabe ba amma shi yayi nasara a zaben gaske
  • Hukumar shirya da zabe ta kasa INEC na shirin gudanar da zaben shugaban kasa ranar 28 ga Febrairu 2023

Majalisar yakin neman zaben jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta yi watsi da zaben yanar gizo dake nuna cewa Peter Obi na jam'iyyar Labour Party LP ya fi karbuwa wajen jama'a.

Dirkatan yada labaran majalisar, Bayo Onanuga, ya tuhumci kungiyar NOI da ta yi binciken da son kai da kuma wallafa karya, rahoton ChannelsTV.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Bincike ya nuna wanda zai iya lashe zabe tsakanin 'yan takarar shugaban kasa 4

A jawabin da ya fitar, Onanuga yace:

"NOI ta zabi wani dan takara kuma ta shirya binciken karya don tallatawa yan Najeriya."
"Ko a jikinmu wannan labarin karyan saboda bincikenmu ya nuna cewa kungiyar NOI ta dade tana zaben karya a lokacin zabe."
Yan Takara
Duk Karya Ce, APC Tayi Watsi Da Zaben Yanar Gizo Na Cewa Peter Obi Yafi Samun Karbuwa Hoto: Peoples Gazzete
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Onanuga yace haka a shekarar 2015 NOI tace Goodluck Jonathan zai lashe zaben amma daga baya shugaba Buhari ne ya lashe.

"Jam'iyyarmu na iyakar kokarinta wajen lashe zabuka a fadin tarayya da tazara mai fadi da ko kotu ya adawa ba zasu iya zuwa ba," ya kara.

Wani Bincike Ya Nuna Peter Obi Ya Fi Sauran ’Yan Takarar Shugaban Kasa Karbuwa a Zaben 2023

Mun kawo muku cewa zaben bincike da ANAP Foundation ta gudanar a wannan watan, ya nemi ra'ayin jama'a kan fitattun 'yan takarar shugaban kasa na APC; Bola Tinubu, PDP; Atiku Abubakar da NNPP; Rabiu Musa Kwankwaso.

Kara karanta wannan

Babu Wani Kulumboto da Sihiri da APC Zata yi Amfani da Shi Don Cin Zabe, Ortom

Rabiu Musa Kwankwaso na NNPP ne ya zo na hudu tare da Obi a farko, Tinubu da Atiku kuwa suka yi kunnen doki.

Za dai a kada kuri'u a zaben 2023 mai zuwa nan da watan Fabrairun shekarar mai zuwa ga rabon ganin badi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel