Kuma dai, Kotu Ta Dage Zaman Gwamnati Da ASUU Zuwa Ranar Litinin

Kuma dai, Kotu Ta Dage Zaman Gwamnati Da ASUU Zuwa Ranar Litinin

Kotun Ma'aikata Ta Kasa ta dage zaman karar da gwamnatin tarayya ta shigar kan kungiyar Malaman Jami'a (ASUU) zuwa ranar Litinin 19 ga Satumba, 2022.

A zaman da akayi ranar Juma'a, lauyan Gwamnati, James Igwe, ya bukaci kotu ta gaggauta yanke hukunci kan wannan lamari saboda muhimmancinsa don dalibai su koma makaranta.

Igwe ya bayyana kotu cewa tunda yanzu ana shari'a, ya kamata Malamai su janye daga yajin aiki zuwa ranar yanke hukunci, rahoton ChannelsTV.

Da dumi
Kuma dai, Kotu Ta Dage Zaman Gwamnati Da ASUU Zuwa Ranar Litinin
Asali: Original

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel