Yadda Aka Titsiye Shugaban PSC, aka Tirsasa shi Yayi Murabus ana Tsaka da Taro

Yadda Aka Titsiye Shugaban PSC, aka Tirsasa shi Yayi Murabus ana Tsaka da Taro

  • A ranar Laraba ne shugaban hukumar kula da ayyukan 'yan sanda, Musiliu Smith yayi murabus daga mukaminsa
  • An gano cewa, an zauna taron hukumar ne inda wasu daga cikin kwamishinoni suka bukacesa da yayi murabus don samun damar zaman hukumar da kanta
  • Hargitsi da rikici ya fara a hukumar tun makonnin da suka gabata inda ake zargin almundahanar kudade, rikicin daukar aiki da yajin aikin wasu ma'aikatan hukumar

FCT, Abuja - Tsohon sifeta janar na ‘yan sandan Najeriya, Musiliu Smith, a jiya Laraba yayi murabus daga matsayinsa na shugaban hukumar kula da harkokin ‘yan sanda bayan rikicin da ya barke a hukumar.

Majiyoyi sun ce a taron shugabannin PSC da aka yi ranar Laraba, an bukaci Smith da yayi murabus kuma ya mika ragamar hukumar hannun mai shari’a Clara Ogunbiyi mai ritaya wacce ke wakiltar fannin shari’a a hukumar.

Kara karanta wannan

Sanatoci Za Su Kashe Ma’aikatu, Cibiyoyi da Hukumomin Gwamnati 400 a shekarar 2023

Musiliu Smith
Yadda Aka Titsiye Shugaban PSC, asak Tirsasa shi Yayi Murabus ana Tsaka da Taro. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Ogunbiyi zata shugabanci hukumar a matsayin mukaddashi kafin shugaba Muhammadu Buhari ya nada sabon shugaban.

Mai magana da yawun hukumar, Ikechukwu Ani, ya tabbatar da murabus din Smith amma ya ki yin karin bayani a kai.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Daily Trust ta rahoto cewa, ayyukan hukumar sun gurgunce tun makonni kadan da suka gabata bayan yajin aikin sai baba ta gani da wasu ma’aikatan hukumar suka fada sakamakon wasu bukatunsu da aka gaza biya wanda ya hada da karbe ragamar dibar kananan ‘yan sanda aiki da ‘yan sanda suka yi, karin girman ma’aikata da horarwa daga hukumar.

Ma’aikatan sun kara da zargin waddaka da kudaden da aka ware domin yi ofishin dindindin na hukumar.

Majiyoyi sun bayyana cewa, taron ya tattauna kan yuwuwar gyara dokar PSC har da cire sashen da yace shugaban hukumar dole ya kasance sifeta janar na ‘yan sanda da yayi murabus.

Kara karanta wannan

Mun Gaji Da Kashe Mana Mazaje Da Makiyaya Ke Yi: Mata Sun Yi Zanga-Zanga A Jihar Arewa, Sun Tare Titi

“Ana fara taron, daya daga cikin kwamishinonin yace hukumar ta farar hula ce ba a cikin ‘yan sanda take ba. Wannan yasa akwai dacewa idan PSC ta kasance mai zaman kanta. Ba za ta kasance hakan ba kuwa idan tsohon sifeta janar na ‘yan sanda ke shugabantarta.
“Bayan tattaunawa, wani kwamishinan ya bukaci Smith da yayi murabus inda wani kwamishinan ya amince da hakan tare da goyon baya.”

- majiyar tace.

Wata majiyar tace, bayan Smith ya amince da yin murabus, an dakatar da taron har sai hukumar ta yi sabbin shugabannni sannan zata cigaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng