Mun Gaji Da Kashe Mana Mazaje Da Makiyaya Ke Yi: Mata Sun Yi Zanga-Zanga A Jihar Arewa, Sun Tare Titi

Mun Gaji Da Kashe Mana Mazaje Da Makiyaya Ke Yi: Mata Sun Yi Zanga-Zanga A Jihar Arewa, Sun Tare Titi

  • Matan aure a garin Filiya da ke karamar hukumar Shongom a Jihar Gombe sun fito sun yi zanga-zangar lumana a ranar Laraba kan kisar mazajensu
  • Matan, wadanda suka tare hanyar shiga garin sun koka cewa makiyaya suna halaka musu mazaje tare da cinye musu amfani gona kuma hukuma ba ta daukan mataki
  • Masu zanga-zangar sun yi kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da abin ya rataya a kansu da su kawo karshen rikicin da ke janyo asarar rayyuka da dukiyoyi

Jihar Gombe - Wasu matan daga garin Filiya, a karamar hukumar Shongom, Jihar Gombe, a ranar Laraba sun yi zanga-zangan lumana bayan kisar da ake zargin makiyaya sun yi wa mazajensu.

Rundunar yan sandan Najeriya reshen jihar Gombe ta tabbatar an kashe mutum 11 sannan an kona gidaje 11 a harin baya-bayan nan a Kushi.

Kara karanta wannan

Taraba: Dubban jama'a sun yi wa Nyame maraba bayan Buhari yayi masa rangwame

Mata Masu Zanga-Zanga
Mata A Wata Jihar Arewa Sun Tare Titi, Suna Zanga-Zangar Kashe Musu Mazaje Da Makiyaya Ke Yi. Hoto: @MobilePunch.
Asali: Twitter

The Punch ta rahoto cewa matan da suka yi zanga-zangan sun rufe hanyar zuwa garin suna cewa sun aikata hakan ne don nuna damuwar, sun kuma ce ba su gamsu da matakan da gwamnati ta dauka ba.

Koken matan na garin Kushi a Gombe

A cewarsu:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Munyi hakan ne saboda shiru da dagacin garin mu da mahukunta suka yi da kuma rashin kawo karshen rikicin makiyaya/manomaa da ya halaka mazajen mu. Shanun makiyaya sun cinye amfanin gonar mu ba mu da abinci."

Matan, yayin da suke kokawa kan wahalhalun da suke sha, sun yi bayanin cewa hare-haren sun karu, suna kiran a warware matsalar tsaron cikin gaggawa.

Matan da ke zanga-zanga sun kara da cewa:

"A makon da ta gabata, an kashe wani a gonarsa, an yanki wani da adda, wasu yaran makiyaya sun far mana a gona a safiyar yau, Allah ne ya bamu ikon tserewa."

Kara karanta wannan

Za a Gurfanar da Mamu a Gaban Kotu, DSS ta Haramtawa Lauyoyi da 'Yan Uwansa Ganinsa

Martanin yan sandan Gombe

Da aka tuntube shi, kakakin yan sandan Jihar Gombe, ASP Mahid Abubakar, ya yi alkawarin zai yi bincike kafin ya yi magana.

Amma, har zuwa lokacin hada wannan rahoton, Abubakar bai riga ya fitar da wata sanarwa ba.

Ba Makiyaya Fulani Ke Kisa Ba, Baƙi Ne Suka Shigo Nigeria, Gwamna Ikpeazu

A wani rahoton, Okezie Ikpeazu, gwamnan jihar Abia ya ce wasu mutane daga kasashen waje ne ke kashe kashe a Nigeria ba makiyaya Fulani bane, The Cable ta ruwaito.

Gwamnan ya yi wannan furucin ne yayin da ya ke magana da manema labarai a Abuja a ranar Alhamis yayin ziyarar da ya kai gidan talabijin na TOS.

Asali: Legit.ng

Online view pixel